Ta Hannun Matiyu 16:1-28

  • An ce Yesu ya nuna alama (1-4)

  • Yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa (5-12)

  • Mabuɗan Mulkin sama (13-20)

    • Gina ikilisiya a kan dutse (18)

  • Yesu ya ce za a kashe shi (21-23)

  • Almajiran Yesu na gaske (24-28)

16  Sai Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo wurinsa domin su gwada shi, sun ce masa ya nuna musu wata alama daga sama. 2  Sai ya amsa ya ce musu: “Idan yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau don sama ta yi ja.’ 3  Da safe kuma kukan ce, ‘Za a yi sanyi da ruwan sama a yau domin sama ta yi ja, kuma hadari ya haɗu.’ Kun iya gane yanayin sararin sama amma ba ku iya gane alamun wannan zamanin ba. 4  Mutanen zamanin nan mugaye ne kuma marasa aminci, sun ci-gaba da son a nuna musu wata alama, amma ba za a nuna musu alama ba, sai dai alamar Yunana.” Bayan haka, sai ya tafi ya bar su. 5  Almajiransa sun haye zuwa ɗayan gefen tekun, amma sun manta su ɗauki burodi. 6  Sai Yesu ya ce musu: “Ku buɗe idanunku kuma ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 7  Sai suka soma magana da junansu suna cewa: “Ai, ba mu ɗauko burodi ba.” 8  Da Yesu ya ji haka, ya ce musu: “Me ya sa kuke magana da juna cewa ba ku ɗauko burodi ba, ku masu ƙarancin bangaskiya? 9  Har yanzu ba ku gane ba, kun manta da yadda na ciyar da maza dubu biyar da burodi biyar, kuma kwanduna nawa kuka tattara? 10  Ko kuma lokacin da na ciyar da maza dubu huɗu da burodi bakwai, manyan kwanduna nawa ne kuka tattara? 11  Yaya aka yi ba ku gane cewa ba burodi nake magana a kai ba? Amma ina nufin ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 12  Sai suka gane cewa ba yistin burodi ba ne yake nufi, amma yana nufin su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa. 13  Saꞌad da ya shigo yankin Kaisariya Filibi, Yesu ya tambayi almajiransa ya ce: “Wane ne mutane suke cewa shi ne Ɗan mutum?” 14  Suka ce masa: “Wasu sun ce Yohanna Mai Baftisma ne, wasu kuma sun ce Iliya. Har ila, wasu sun ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.” 15  Sai ya ce musu: “Ku kuma fa, a ganinku, ni wane ne?” 16  Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce masa: “Kai ne Kristi, Ɗan Allah mai rai.” 17  Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Ka yi farin ciki,* Siman ɗan Yunana, domin ba mutum* ba ne ya bayyana maka hakan, amma Ubana ne da ke sama ya bayyana maka. 18  Ina kuma gaya maka: Kai ne Bitrus, a kan wannan dutse ne zan gina ikilisiyata, kuma ƙofofin Kabari ba za su fi ƙarfinta ba. 19  Zan ba ka mabuɗan Mulkin sama, kuma duk abin da ka ɗaure a duniya zai zama abin da aka ɗaure a sama. Kuma duk abin da ka kunce a nan duniya, zai zama abin da aka kunce a sama.” 20  Sai ya ja wa almajiransa kunne sosai kada su gaya wa kowa cewa shi ne Kristi. 21  Tun daga lokacin, Yesu ya soma bayyana wa almajiransa cewa, dole ya je Urushalima kuma ya sha wahala sosai daga hannun dattawa, da manyan firistoci, da marubuta, kuma a kashe shi, amma a rana ta uku za a ta da shi. 22  Sai Bitrus ya ja shi gefe ya soma tsawata masa yana cewa: “Ubangiji, kada ka yi wa kanka irin wannan fatan; wannan abin ba zai taɓa faruwa da kai ba.” 23  Amma, Yesu ya juya baya ya ce masa: “Ka rabu da ni Shaiɗan! Kai abin tuntuɓe ne a gare ni domin kana tunani kamar mutum ne ba kamar Allah ba.” 24  Sai Yesu ya ce wa almajiransa: “Duk wanda yake so ya bi ni, sai ya ƙi kansa, kuma ya ɗauki gungumen azabarsa* ya ci-gaba da bi na. 25  Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai sake rayuwa. 26  A gaskiya, mece ce ribar mutum in ya sami dukan duniyar nan amma ya rasa ransa? Ko kuma mene ne mutum zai bayar a maimakon ransa? 27  Domin Ɗan mutum zai zo a cikin ɗaukakar Ubansa tare da malaꞌikunsa kuma zai ba kowa lada bisa ga aikinsa. 28  A gaskiya ina gaya muku, akwai wasu da suke tsaye a nan da ba za su taɓa mutuwa ba har sai sun ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin Mulkinsa.”

Hasiya

Ko kuma “Kai mai albarka ne.”
A yaren Girka, “nama da jini.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.