Ta Hannun Matiyu 1:1-25
1 Littafin tarihin* Yesu Kristi,* ɗan Dauda, ɗan Ibrahim:
2 Ibrahim ya haifi Ishaku;Ishaku ya haifi Yakubu;Yakubu ya haifi Yahuda da ꞌyanꞌuwansa;
3 Yahuda ya haifi Ferez da Zera, kuma Tama ce mahaifiyarsu;Ferez ya haifi Hezron;Hezron ya haifi Ram;
4 Ram ya haifi Amminadab;Amminadab ya haifi Nashon;Nashon ya haifi Salmon;
5 Salmon ya haifi Bowaz, kuma Rahab ce mahaifiyarsa;Bowaz ya haifi Obed, kuma Rut ce mahaifiyarsa;Obed ya haifi Jessi;
6 Jessi ya haifi Dauda wanda ya zama sarki.
Dauda ya haifi Sulemanu, kuma mahaifiyarsa matar Uriya ce a dā;
7 Sulemanu ya haifi Rehobowam;Rehobowam ya haifi Abijah;Abijah ya haifi Asa;
8 Asa ya haifi Jehoshafat;Jehoshafat ya haifi Jehoram;Jehoram ya haifi Uzziya;
9 Uzziya ya haifi Jotam;Jotam ya haifi Ahaz;Ahaz ya haifi Hezekiya;
10 Hezekiya ya haifi Manasse;Manasse ya haifi Amon;Amon ya haifi Josiya;
11 Josiya ya haifi Jekoniya da ꞌyanꞌuwansa. An haife su a lokacin da aka kai Yahudawa bauta a Babila.
12 Bayan da aka kai Yahudawa bauta a Babila, Jekoniya ya haifi Sheyaltiyel;Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel;
13 Zerubbabel ya haifi Abihud;Abihud ya haifi Eliyakim;Eliyakim ya haifi Azoh;
14 Azoh ya haifi Zadok;Zadok ya haifi Akim;Akim ya haifi Eliyud;
15 Eliyud ya haifi Eleyaza;Eleyaza ya haifi Mattan;Mattan ya haifi Yakubu;
16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kristi.
17 Dukan tsara daga Ibrahim zuwa Dauda, tsara goma sha huɗu ne; daga Dauda zuwa lokacin da aka kai Yahudawa bauta a Babila, tsara goma sha huɗu ne; daga lokacin da aka kai Yahudawa bauta a Babila zuwa lokacin Kristi, tsara goma sha huɗu ne.
18 Ga abin da ya faru kafin a haifi Yesu Kristi. A lokacin da Yusufu ya yi wa Maryamu mahaifiyar Yesu alkawarin aure, an gano cewa Maryamu ta ɗauki ciki ta wurin ruhu mai tsarki kafin a yi musu auren.
19 Amma da yake mijinta Yusufu mai aminci ne, kuma ba ya so ya kunyatar da ita, ya yi shirin fasa auren a ɓoye.
20 Bayan da ya yi tunani a kan abubuwan nan, sai malaꞌikan Jehobah* ya gaya masa a mafarki cewa: “Yusufu, ɗan Dauda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu ta zama matarka. Domin ruhu mai tsarki ne ya sa ta ɗauki cikin.
21 Za ta haifi ɗa, kuma za ka sa masa suna Yesu,* domin zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
22 Dukan abubuwan nan sun faru ne don su cika abin da Jehobah* ya faɗa ta wurin annabinsa cewa:
23 “Ga shi kuwa! Budurwar za ta yi ciki, za ta haifi ɗa, kuma za a ba shi suna Immanuwel,” wanda idan aka fassara yana nufin, “Allah Yana Tare da Mu.”
24 Sai Yusufu ya farka daga barci, ya yi abin da malaꞌikan Jehobah* ya ce ya yi, kuma ya ɗauki matarsa ya kai ta gidansa.
25 Amma bai kwana* da ita ba har sai bayan da ta haifi ɗa, kuma ya ba wa ɗan suna Yesu.
Hasiya
^ Ko kuma “zuriyar.”
^ Ko kuma “Almasihu; Shafaffe.”
^ An rubuta sunan Allah, wato Jehobah, sau 237 a Nassosin Girkanci na Kirista, kuma wannan ne karo na farko da sunan ya bayyana a juyin nan. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Sunan nan yana da maꞌana ɗaya da sunan Ibranancin nan Jeshuwa ko kuma Joshuwa, maꞌanar ita ce, “Jehobah Mai Ceto Ne.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “yi jimaꞌi.”