Ta Hannun Luka 3:1-38

  • Lokacin da Yohanna ya soma hidimarsa (1, 2)

  • Yohanna yana gaya wa mutane su yi baftisma (3-20)

  • An yi wa Yesu baftisma (21, 22)

  • Tarihin Yesu Kristi (23-38)

3  A cikin shekara ta goma sha biyar na mulkin Kaisar Tiberiyus, saꞌad da Buntus Bilatus ne gwamnan Yahudiya, Hirudus* yana mulkin yankin Galili, ɗanꞌuwansa Filibus yana mulkin ƙasar Ituriya da Tarakunitas, kuma Lisaniyas ne yake mulkin yankin Abilene, 2  a kwanakin Kayafas da babban firist Anas, sai Allah ya ba wa Yohanna ɗan Zakariya saƙo saꞌad da Yohanna yake daji. 3  Sai Yohanna ya je dukan garuruwa da ke kewaye da Kogin Jodan, yana waꞌazi cewa mutane su yi baftisma. Hakan zai nuna cewa sun tuba don a gafarta zunubansu, 4  kamar yadda aka rubuta a littafin annabi Ishaya cewa: “Wata murya tana kira a daji tana cewa: ‘Ku shirya hanyar Jehobah!* Ku sa hanyoyinsa su miƙe. 5  A ciccika kowane kwari, a kwantar da kowane ƙaramin tudu da kuma kowane babban tudu, a miƙe hanyar da take da kwana-kwana, a gyara mummunar hanya ta yi kyau. 6  Kuma kowa zai ga yadda Allah zai ceci mutane.’” 7  Sai Yohanna ya soma ce wa jamaꞌar da suke zuwa don ya yi musu baftisma: “Ku ꞌyaꞌyan macizai masu dafi, wa ya gargaɗe ku ku guje wa hukuncin nan da ke zuwa? 8  Saboda haka, ku yi abubuwan da za su nuna cewa kun tuba. Kada ku yi taƙama cewa, ‘Ibrahim babanmu ne.’ Domin ina gaya muku cewa Allah zai iya ta da wa Ibrahim ꞌyaꞌya daga duwatsun nan. 9  Hakika, an riga an sa gatari a ƙarƙashin itatuwan. Saboda haka, duk wani itace da ba ya ba da ꞌyaꞌya masu kyau, za a sare shi, a jefa a cikin wuta.” 10  Sai jamaꞌar suka yi ta tambayar sa cewa: “To mene ne ya kamata mu yi?” 11  Sai ya amsa ya ce musu: “Bari wanda yake da riguna biyu ya ba wanda ba shi da ko ɗaya. Kuma wanda yake da abinci, shi ma ya yi haka.” 12  Har ma masu karɓan haraji sun zo domin a yi musu baftisma, kuma suna tambayar sa cewa: “Malam, mene ne ya kamata mu yi?” 13  Sai ya ce musu: “Kada ku karɓa fiye da harajin da aka ce ku karɓa.” 14  Sojoji ma suna tambayar sa cewa: “Mene ne ya kamata mu yi?” Kuma ya ce musu: “Kada ku ci zarafin* wani, ko ku yi ma wani zargin ƙarya, amma ku gamsu da abubuwan da kuke da su.” 15  A lokacin, mutanen suna jiran zuwan Kristi, kuma dukansu suna tunani a zuciyarsu game da Yohanna cewa, “Anya ba shi ne Kristi ba kuwa?” 16  Sai Yohanna ya amsa ma dukansu ya ce: “Ni dai da ruwa nake yi muku baftisma, amma wanda yake zuwa ya fi ni ƙarfi, wanda ko igiyar takalmarsa ma ban isa in kunce ba. Shi ne wanda zai yi muku baftisma da ruhu mai tsarki da kuma wuta. 17  Matankaɗensa yana hannunsa, don ya share wurin da yake tankaɗe hatsinsa da kyau. Zai tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙona dusar da wutar da ba za a iya kashewa ba.” 18  Yohanna ya kuma yi gargaɗi da yawa ga mutane kuma ya ci-gaba da yi musu shelar labari mai daɗi. 19  Dā ma Yohanna ya tsawata wa Hirudus mai mulkin yankin, saboda Hirudiya matar ɗanꞌuwan Hirudus, da kuma dukan miyagun ayyuka da Hirudus ya aikata. 20  Hirudus ya ƙara aikata wata mugunta kuma: Ya sa an kulle Yohanna a kurkuku. 21  Bayan da aka yi wa dukan mutanen baftisma, Yesu ma an yi masa baftisma. Yayin da yake adduꞌa, sai sama ya buɗe. 22  Sai ruhu mai tsarki a kamannin kurciya ya sauko a kansa, sai wata murya daga sama ta ce: “Kai Ɗana ne, wanda nake ƙauna, na amince da kai.” 23  Saꞌad da Yesu ya soma hidimarsa, yana wajen shekara talatin, mutane sun san shi a matsayin,ɗan Yusufu,ɗan Heli, 24  ɗan Mattat,ɗan Lawi,ɗan Malki,ɗan Jannai,ɗan Yusufu, 25  ɗan Mattatiya,ɗan Amos,ɗan Nahum,ɗan Esli,ɗan Naggai, 26  ɗan Maat,ɗan Mattatiya,ɗan Simeyan,ɗan Josek,ɗan Joda, 27  ɗan Jowanan,ɗan Resa,ɗan Zerubbabel,ɗan Sheyaltiyel,ɗan Neri, 28  ɗan Malki,ɗan Addi,ɗan Kosam,ɗan Elmadam,ɗan Er, 29  ɗan Yesu,*ɗan Eliyeza,ɗan Jorim,ɗan Mattat,ɗan Lawi, 30  ɗan Simeyon,ɗan Yahuda,ɗan Yusufu,ɗan Jonam,ɗan Eliyakim, 31  ɗan Meleya,ɗan Menna,ɗan Mattata,ɗan Natan,ɗan Dauda, 32  ɗan Jesse,ɗan Obed,ɗan Bowaz,ɗan Salmon,ɗan Nashon, 33  ɗan Amminadab,ɗan Arnai,ɗan Hezron,ɗan Ferez,ɗan Yahuda, 34  ɗan Yakubu,ɗan Ishaku,ɗan Ibrahim,ɗan Tera,ɗan Nahor, 35  ɗan Serug,ɗan Reyu,ɗan Feleg,ɗan Eber,ɗan Shela, 36  ɗan Kenan,ɗan Arfakshad,ɗan Shem,ɗan Nuhu,ɗan Lamek, 37  ɗan Metusela,ɗan Enok,ɗan Jared,ɗan Mahalalel,ɗan Kenan, 38  ɗan Enosh,ɗan Set,ɗan Adamu,ɗan Allah.

Hasiya

Wato, Hirudus Antifas. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “kwace kuɗi da ƙarfi daga.”
Ko kuma “Joses,” kamar yadda yake a wasu rubuce-rubucen da aka yi a yaren Girka.