Koma ka ga abin da ke ciki

7 GA AFRILU, 2016
RASHA

Gwamnati Tana Barazanar Rufe Hedkwatar Shaidun Jehobah a Kasar Rasha

Gwamnati Tana Barazanar Rufe Hedkwatar Shaidun Jehobah a Kasar Rasha

Gwamnatin Kasar Rasha ta aika wa Ofishin Shaidun Jehobah na kasar wasikar gargadi, domin ofishin yana tsara ayyukan addini a kasar. Wadannan ayyukan ibadar su ne Shaidun Jehobah a fadin duniya suke yi, babu tashin hankali. Wasikar, wadda aka rubuta a ranar 2 ga Maris, 2016, kuma mataimakin Alkalin V. Ya. Grin ya sa hannu a ciki ta ce ibadar da Shaidun Jehobah suke yi ta zo daya da “ayyukan tsattsauran ra’ayi” kuma ta umurci Ofishin da ya kawar da wadannan “ayyukan da suka saba wa doka” a cikin watanni biyu, in ba haka ba, gwamnati za ta rufe Ofishin.

Wannan yunkurin rufe hedkwatar Shaidun Jehobah a kasar Rasha mataki ne da gwamnatin kasar take mara wa baya. Tun daga shekara ta 2007, hukumomi a Rasha suna amfani da dokar Kasar Rasha a kan tsattsauran ra’ayi su takura wa Shaidun Jehobah, har ma a wasu wurare sun wargaje kungiyoyinsu kuma sun haramta littattafansu na addini da yawa.