29 GA SATUMBA, 2020
RASHA
Alkali Ya Mayar da Karar da Aka Shigar a Kan ’Yar’uwa Yelena Barmakina Domin Babu Hujjar da Ta Goyi Bayan Zargin
A ranar 29 ga Satumba, 2020, Kotun Gundumar Pervorechenskiy da ke birnin Vladivostok ya ki ya yanke hukunci a kan karar da aka shigar da ta shafi ’Yar’uwa Yelena Barmakina. A maimakon haka, kotun ya mayar da karar ga wanda suka shigar da ita. Alkali ya bayyana cewa babu wata hujja da ta isa ta goyi bayan zargin da suke yi wa ’Yar’uwa Barmakina cewa ta yi ayyukan masu tsattsauran ra’ayi. Wadanda suka shigar da karar za su iya daukaka kara. Ko kuma a dakatar da wannan karar har sai sun samo hujjar da ta isa ta sa a saurari karar.