26 GA AFRILU, 2017
FILIFIN
Shaidun Jehobah Sun Dauki Matakin Gyara Gidaje Bayan Wata Mahaukaciyar Guguwar Super Typhoon Nock-Ten Ta Yi Barna
MANILA, Filifin—Shaidun Jehobah a kasar Filifin sun soma wata gagarumar aikin gyara da kuma gina gidajen da mahaukaciyar guguwar typhoon nock-ten (da suke kira“Nina”) ta lalatar.
A ranar 25 ga Disamba, 2016, mahaukaciyar guguwar ta yi kaca-kaca da yankin Bicol. Rahoto da aka samo ya nuna cewa guguwar ta halaka mutane goma da kuma gidaje fiye da 390,000. Babu wani cikin Shaidun Jehobah da ya mutu ko kuma ji wani rauni mai tsanani a yankin. Amma gidajen Shaidun fiye da 300 da kuma wuraren ibadarsu (da ake kira Majami’un Mulki) 24 ne suka lalace ko kuma halaka. Ofishin Shaidun Jehobah da ke Filifin ya kafa kwamitin aikin kayan agaji a Birnin Naga don su taimaka wa iyalin Shaidun Jehobah da bala’in ya shafa.
Dean Jacek kakakin Shaidun Jehobah da ke Filifin ya ce: ‘A yanzu dai, Shaidun da suka ba da kai don ba da agaji sun gyara gidaje 271 na ‘yan’uwa da kuma Majami’un Mulki 22. Za su ci gaba da tallafa wa da kuma gyare-gyaren sauran gidaje 38 da Majami’un Mulki 2 da suke rage. Muna fatan cewa za su kammala aikin a karshen watan Afrilu, 2017.
Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne ke kula da aikin Shaidun Jehobah a fadin duniya da kuma amfani da gudummawar da ake bayarwa wajen tanadin kayan agaji. A cikin Shaidun Jehobah fiye da miliyan 8 da ke fadin duniya, Shaidu sama da 209,000 ne ke Filifin.
Media Contacts:
International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000
Philippines: Dean Jacek, +63-2-224-4444