Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Biyan Zakka?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Allah ya dokaci Israꞌilawa su rika ba da zakka a kowace shekara don su tallafa wa ayyukan ibada. Allah ya ce musu: “Lallai za ku fitar da zakka ta dukan amfanin da kuka shuka a gonakinku kowace shekara.”—Maimaitawar Shariꞌa 14:22.
Ba da zakka yana cikin dokokin da Allah ya ba wa Israꞌilawa a dā. Kiristoci a yau ba sa karkashin dokar da Allah ya ba wa Israꞌilawa, don haka, ba dole ba ne su ba da zakka. (Kolosiyawa 2:13, 14) A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce kowane Kirista ya yi gudummawa “kamar yadda ya yi niyya, ba tare da bacin rai ko tilas ba, domin Allah yana son mai bayarwa da dadin rai.”—2 Korintiyawa 9:7.
Yadda Aka Ba da Zakka a dā a Littattafan “Tsohon Alkawari”
An ambaci kalmar nan zakka a wurare da yawa a littattafan da mutane da yawa suke kira Tsohon Alkawari. Kuma yawancin wadannan ayoyin sun yi magana ne a kan lokacin da Israꞌilawa suke karkashin Dokar da Allah Ya Bayar ta Hannun Musa (Dokar Musa). Amma akwai wurare biyu a Littafi Mai Tsarki da aka ambaci zakka kafin ma wannan lokacin.
Kafin Dokar Musa
Mutum na farko da Littafi Mai Tsarki ya ce ya ba da zakka shi ne Abram (Ibrahim). (Farawa 14:18-20; Ibraniyawa 7:4) Da alama cewa sau daya ne Abram ya ba da wannan zakkar ga sarkin Salem wanda shi ma firist ne a lokacin. Littafi Mai Tsarki bai ce Ibrahim ko ꞌyaꞌyansa sun sake ba da zakka ba.
Mutum na biyu da Littafi Mai Tsarki ya ce ya ba da zakka shi ne jikar Ibrahim mai suna Yakubu. Ya yi alkawari cewa idan Allah ya albarkace shi, zai ba da “zakka.” (Farawa 28:20-22) Wasu masanan Littafi Mai Tsarki sun ce watakila zakkar da Yakubu ya bayar hadayun dabbobi ne. Ko da yake Yakubu ya yi alkawari cewa zai ba da zakka, bai ce wa ꞌyan iyalinsa su ma su rika ba da zakka ba.
Bisa Dokar Musa
An umurci Israꞌilawa a dā su rika ba da zakka don a tallafa wa ayyukan ibada da ita.
Da zakkar da Israꞌilawa suke bayarwa ne ake kula da Lawiyawa da firistoci da aikinsu musamman shi ne yin ayyukan ibada. Ba a ba wadannan mutanen gonar da za su rika nomewa. (Littafin Kidaya 18:20, 21) Idan Lawiyawa da ba firistoci ba suka karbi zakka daga jamaꞌar Israꞌila, sukan cire ‘zakka daga cikinta’ su ba ꞌyanꞌuwansu Lawiyawa da firistoci.—Littafin Kidaya 18:26-29.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai wata zakka kuma da Israꞌilawa suka bayar a dā. An yi amfani da wannan zakkar don a tallafawa Lawiyawa da wadanda ba Lawiyawa ba. (Maimaitawar Shariꞌa 14:22, 23) Wannan zakkar ce Israꞌilawa suka yi amfani da ita a lokacin wasu bukukuwansu na ibada. Kuma akwai shekarun da ake amfani da wannan zakkar don a taimaka wa talakawa su sami abin biyan bukata.—Maimaitawar Shariꞌa 14:28, 29; 26:12.
Yaya Israꞌilawa suke lissafin zakka da za su bayar? Israꞌilawa sukan ba da kashi daya cikin goma na amfanin gona da suka samu a shekara. (Littafin Firistoci 27:30) Idan kudi ne za su bayar a maimakon amfanin gonarsu, za su dan ba da fiye da kashi daya cikin goma. (Littafin Firistoci 27:31) An kuma umurce su su ba da “zakka ta garke, ko ta shanu, ko ta tumaki ko ta awaki.”—Littafin Firistoci 27:32.
Don su san dabbobin da za su ba da su zakka, Israꞌilawa sukan kirga dabbobinsu kuma idan suka kai kan na goma sai su ba da ita zakka. Dokar ta ce, na goman nan ne za a bayar, ko da karama ce ko babba, ko tana ciwo ko ba ta ciwo. Ba za su iya sayar da dabbar kuma su ba da kudin a matsayin zakka ba. (Littafin Firistoci 27:32, 33) Amma idan aka zo ga zakka ta biyu da ake amfani da ita a lokacin bukukuwansu, za su iya sayar da dabbobin kuma su ba da kudin. Hakan ya sa abubuwa sun yi ma Israꞌilawan sauki da yake sukan yi tafiya mai nisan gaske kafin su isa inda ake bukukuwan.—Maimaitawar Shariꞌa 14:25, 26.
A wane lokaci ne Israꞌilawa suke ba da zakka? A kowace shekara, Israꞌilawa suna ba da zakka. (Maimaitawar Shariꞌa 14:22) Amma a shekara ta bakwai ba sa ba da zakka. Domin shekara ta bakwai, shekara ta cikakken hutu ce, Israꞌilawa ba sa noma. (Littafin Firistoci 25:4, 5) Wannan dalilin ne ya sa Israꞌilawa ba sa ba da zakka a wannan shekarar. Kafin shekara ta bakwai, wato wannan shekarar hutun, Allah ya ce su ba da zakka, ta shekara ta uku da ta shida ga talakawa da kuma Lawiyawa.—Maimaitawar Shariꞌa 14:28, 29.
Shin ana hukunta mutum idan bai ba da zakka ba? Dokar Musa ba ta ambata wani hukunci da za a yi wa mutumin da ya ki ba da zakka ba. Suna ba da zakka don su faranta wa Allah rai ne ba wai don su guje ma wani hukunci ba. Bayan Israꞌilawan sun ba da zakkar, Allah ya umurce su su fada a gaban shi cewa sun ba da zakkar saꞌan nan su roke shi ya musu albarka don abin nan da suka yi. (Maimaitawar Shariꞌa 26:12-15) Allah ya ce wadanda suka ki ba da zakka kamar sata suke masa.—Malakai 3:8, 9.
Zakkar ta fi karfinsu ne? Aꞌa. Allah ya yi wa Israꞌilawan alkawari cewa idan sun ba da zakka, zai zubo musu da albarka kuma ba za su rasa kome ba. (Malakai 3:10) Amma idan Israꞌilawan suka ki ba da zakka, sukan sha wahala ba kadan ba. Allah ba ya musu albarka. Kuma kin ba da zakka yakan sa firistoci da Lawiyawa su koma neman abin da za su ci, maimakon su taimakawa Israꞌilawa su kusaci Allah.—Nehemiya 13:10; Malakai 3:7.
Yadda Aka Ba da Zakka a dā a Littattafan “Sabon Alkawari”
Har a lokacin da Yesu yake duniya ma, Allah ya bukaci bayinsa su ba da zakka. Amma bayan da Yesu ya mutu, an kawar da wannan dokar.
A zamanin Yesu
A nassosin da mutane suke kira Sabon alkawari, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Israꞌilawa sun ci gaba da ba zakka a lokacin da Yesu yake duniya. Yesu ya ce zakka da suke biya ya dace, amma ya yi fushi da malaman addini da suke biyan zakka amma sun “kyale abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin dokoki, wato gaskiya, da jin kai, da aminci.”—Matiyu 23:23.
Bayan mutuwar Yesu
Ba a bukaci bayin Allah su ba da zakka bayan mutuwar Yesu ba. Domin hadayar da Yesu ya bayar ya share ko kawar da Dokar Musa hade da dokar nan ta karban zakka daga hannun jama’a.—Ibraniyawa 7:5, 18; Afisawa 2:13-15; Kolosiyawa 2:13, 14.
a Zakka tana nufin “kashi daya cikin goma na abubuwan da mutum yake samuwa kowace shekara da yake kebewa don yin wani abu na musamman. Zakka da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ana amfani da ita ne don ibada.”—In ji littafin nan Harper’s Bible Dictionary, shafuffuka na 765.