Shin Littafi Mai Tsarki Ya Koyar da Yin Rayuwa a Wani Wuri Bayan Mutuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a, bai koyar da hakan ba. Babu wannan furucin a cikin Littafi Mai Tsarki. Koyarwar yin rayuwa a wani wuri bayan mutuwa ta samo asali ne daga koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa. a Amma Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa kurwa ita ce ainihin mutumin kuma tana mutuwa. (Farawa 2:7; Ezekiyel 18:4) Idan mutum ya mutu, ba zai iya yin kome ba.—Farawa 3:19; Mai-Wa’azi 9:5, 6.
Mene ne bambancin koyarwar yin rayuwa a wani wuri bayan mutuwa da kuma tashin matattu?
Koyarwar Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu ba ta samo asali daga koyarwar kurwa marar mutuwa ba. A lokacin da za a yi tashin matattu, Allah zai yi amfani da ikonsa don ya ta da mutanen da suka mutu. (Matta 22:23, 29; Ayyukan Manzanni 24:15) Begen tashin matattu ya sa mun kasance da begen cewa za a ta da mutane zuwa sabuwar duniya kuma ba za su sake mutuwa ba.—2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
Ra’ayin da bai dace ba game da yin rayuwa a wani wuri bayan mutuwa da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
Kage: Littafi Mai Tsarki ya ce Iliya ne ya dawo rayuwa a matsayin Yohanna Mai Baftisma.
Gaskiya: Allah ya ce: “Zan aike muku annabi Iliya,” kuma Yesu ya ce Yohanna Mai Baftisma ne ya cika wannan annabcin. (Malakai 4:5, 6; Matta 11:13, 14) Amma wannan ayar ba ta nuna cewa Iliya ne ya dawo rayuwa a matsayin Yohanna Mai Baftisma ba. Yohanna da kansa ya ce shi ba Iliya ba ne. (Yohanna 1:21) A maimakon haka, Yohanna ya yi irin wa’azin ceto da Iliya ya yi. (1 Sarakuna 18:36, 37; Matta 3:1) Ban da haka ma, Yohanna ya zama mai “ruhu da iko irin na Iliya.”—Luka 1:13-17, Littafi Mai Tsarki.
Kage: Sake haihuwa da Littafi Mai Tsarki ya ambata yana nufin sake haifan mutum bayan ya mutu.
Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sake haihuwa tana faruwa ne sa’ad da mutum yake raye kuma ba ya faruwa a zahiri. (Yohanna 1:12, 13) Kuma wannan sake haihuwa ba sakamakon abubuwan da mutum ya yi a dā ba ne, amma albarka ce da Allah yake yi wa mutanen da suke da begen yin rayuwa a nan gaba.—Yohanna 3:3; 1 Bitrus 1:3, 4.
a Koyarwar kurwa marar mutuwa da kuma yin rayuwa a wani wuri bayan mutuwa sun samo asali daga Babila ta dā. Bayan haka, sai ’yan falsafa na Indiya suka kirkiro koyarwar nan Karma, wato duk abin da mutum ya yi yana bin sa. Bisa ga Kundin Sanin nan Britannica Encyclopedia of World Religions, wata koyarwa da ake kira Karma a addinin Hindu ta ce, “a Lahira, mutum zai girbi duk abin da ya yi a wannan duniyar.”—Shafi na 913.