Koma ka ga abin da ke ciki

Ina So In Mutu​—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min Idan Ina Tunanin Kashe Kaina?

Ina So In Mutu​—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min Idan Ina Tunanin Kashe Kaina?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kwarai kuwa! Domin “Allahn da yake karfafa wanda ya fid da zuciya” ne ya ba mu Littafi Mai Tsarki. (2 Korintiyawa 7:6) Littafi Mai Tsarki ba littafi mai dauke da bayani game da lafiyar kwakwalwa ba ne. Amma ya taimaka wa mutane da dama su daina tunanin kashe kansu. Kai ma za ka iya amfana.

 Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya bayar?

  • Ka gaya wa wadansu yadda kake ji.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abokin kirki yana nuna kauna a koyaushe kuma shi dan’uwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.”​—Karin Magana 17:​17, New World Translation.

     Abin da hakan yake nufi: Idan muna bakin ciki, muna bukatar wasu su taimaka mana.

     Idan ba ka gaya wa wani abin da yake damunka ba, damuwar za ta iya fin karfinka. Amma idan ka gaya wa wasu yadda kake ji, hakan zai iya rage maka damuwar kuma za ka iya yin tunani da kyau.

     Ga abin da za ka yi: Yau, ka gaya wa wani abokinka ko danginka abin da kake ciki. a Ko kuma ka rubuta yadda kake ji a cikin takarda.

  • Ka je ka ga likita.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.”​—Matiyu 9:12.

     Abin da hakan yake nufi: Ya kamata mu je asibiti idan ba mu da lafiya.

     Idan mutum yana tunanin kashe kansa, hakan ya nuna cewa watakila yana da matsalar kwakwalwa ko ciwon zuciya. Irin wannan rashin lafiyar daya ne da wanda muke yi yau da kullum, don haka ba abin kunya ba ne. Mutanen da ke da matsalar kwakwalwa ko ciwon zuciya za su iya warkewa.

     Ga abin da za ka yi: Ba tare da bata lokaci ba, ka je ka ga likitan da zai iya taimaka maka.

  • Ka tuna cewa Allah ya damu da kai.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba akan sayar da ’yan tsuntsu biyar kobo biyu ba? Duk da haka Allah bai manta da ko dayansu ba . . . Kada ma ku ji tsoro, don kun fi dan tsuntsu daraja barkatai!”​—Luka 12:​6, 7.

     Abin da hakan yake nufi: Kana da daraja a gaban Allah.

     Za ka iya ji kamar ba wanda ya damu da kai, amma Allah yana ganinka kuma ya san yadda kake ji. Ya damu da kai ko da kana ganin rayuwa ta ishe ka. Littafi Mai Tsarki ya ce, “karyayyar zuciya . . . ba za ka rena ta ba, ya Allah.” (Zabura 51:​17, Tsohuwar Hausa a Saukake) Allah yana so ka ci gaba da rayuwa domin yana kaunarka.

     Ga abin da za ka yi: Ka bincika abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya fada da suka nuna cewa Allah yana kaunarka. Alal misali ka karanta Hasumiyar Tsaro Na 3, 2018.

  • Ka yi addu’a ga Allah.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku danka masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”​—1 Bitrus 5:7.

     Abin da hakan yake nufi: Allah yana so ka gaya masa ainihin abin da yake damunka a zuciya.

     Allah zai iya ba ka kwanciyar hankali da kuma karfin jimre yanayinka. (Filibiyawa 4:​6, 7, 13) Wannan wata hanya ce da Allah yake taimakon wadanda suka yi addu’a ya taimaka musu.​—Zabura 55:22.

     Ga abin da za ka yi: Ka yi addu’a ga Allah yau. Ka kira shi da sunansa, wato Yahweh ko Jehobah, kuma ka gaya masa yadda kake ji. (Zabura 83:18) Ka roke shi ya taimaka maka ka ci gaba da jimrewa.

  • Ka yi tunani a kan alkawuran da Allah ya yi mana a Littafi Mai Tsarki game da nan gaba.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wannan sa zuciyar nan tamu tabbatacciya ce mai tsayar da hankalinmu, ba tare da jin tsoro ko yin shakka ba.”​—Ibraniyawa 6:19.

     Abin da hakan yake nufi: Kana iya samun kanka a yanayin da yanzu kana cikin farin ciki, an jima kana cikin bakin ciki kamar jirgin ruwan da igiyar ruwa take tangal-tangal da shi, amma yin tunani a kan alkawuran Allah da muke sa ran morewa a nan gaba zai iya kwantar da hankalinka.

     Wannan begen ba mafarki ba ne. Muna da bege domin Allah ya yi alkawari cewa zai cire duk abubuwan da suke jawo mana azaba.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

     Ga abin da za ka yi: Ka karanta darasi na 5 na kasidar nan, Albishiri Daga Allah! don ka sami karin bayani a kan alkawuran da Allah ya yi game da nan gaba.

  • Ka yi wani abin da kake jin dadin yi.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya mai murna magani ne mai kyau.”​—Karin Magana 17:22.

     Abin da hakan yake nufi: Yin abubuwan da suke sa mu farin ciki zai iya kwantar mana da hankali kuma ya rage mana damuwa.

     Ga abin da za ka yi: Ka yi wani abin da ka saba jin dadinsa. Alal misali, ka saurari wata waka ko ka karanta wani abin da zai karfafa ka, ko kuma ka kama yin wani abin da kake jin dadin yi. Za ka dada yin farin ciki idan ka taimaka wa mutane, ko da dan karamin abu ne ka yi musu.​—Ayyukan Manzanni 20:35.

  • Ka kula da lafiyar jikinka.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wasa jiki tana da amfaninta.”​—1 Timoti 4:​8, Tsohuwar Hausa a Saukake.

     Abin da hakan yake nufi: Mukan amfana sosai idan muka motsa jiki, muka sami isasshen barci, kuma muna cin abinci mai gina jiki.

     Ga abin da za ka yi: Ka fita ka dan taka, ko da na minti 15 ne.

  • Ka tuna cewa yadda muke ji da ma wasu abubuwa a rayuwa sukan canja.

     Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ku ma san me zai faru gobe ba.”​—Yakub 4:14.

     Abin da hakan yake nufi: Mai yiwuwa abin da ke damunka har kana ganin ba mafita, a-kwana-a-tashi zai wuce.

     Ko da halin da kake ciki a yau ya yi muni sosai, abubuwa za su iya canjawa gobe. Don haka ka yi abin da zai taimaka maka ka jimre. (2 Korintiyawa 4:8) Mai yiwuwa da shigewar lokaci matsalar da kake ciki za ta shige, amma idan ka kashe kanka, ba za ka iya dawo da hannun agogo baya ba.

     Ga abin da za ka yi: Ka karanta labaran wadanda suka yi sanyin gwiwa har suka gwammace su mutu a Littafi Mai Tsarki. Za ka ga yadda abubuwa suka canja a rayuwarsu ba tare da sun san cewa hakan zai faru ba. Ga wasu misalai.

 Akwai labaran wadanda suka so su kashe kansu a cikin Littafi Mai Tsarki?

 E. Littafi Mai Tsarki ya ba mu labarin wasu mutane da suka so su mutu. Allah bai yi musu fada ba, a maimakon haka, ya taimaka musu. Kai ma Allah zai iya taimaka maka.

Iliya

  •  Wane ne shi? Iliya annabi ne mai karfin zuciya. Amma akwai wasu lokuta da ya yi sanyin gwiwa. Littafin Yakub 5:17 ta ce, “Iliya mutum ne kamar mu.”

  •  Me ya sa ya so ya mutu? Akwai lokacin da Iliya ya dauka cewa shi kadai ne ya rage, ya ji tsoro kuma ya ga kamar bai da amfani. Shi ya sa ya roki Jehobah ya ce: “Ka dauki raina.”​—1 Sarakuna 19:4.

  •  Me ya taimaka masa? Iliya ya gaya wa Allah yadda yake ji. Me Allah ya yi don ya karfafa shi? Allah ya nuna wa Iliya cewa ya damu da shi kuma ya nuna masa ikonsa. Ya kuma tabbatar wa Iliya cewa har ila yana da daraja kuma ya ba shi mataimaki da zai karfafa shi.

  •  Ka karanta labarin Iliya a: 1 Sarakuna 19:​2-18.

Ayuba

  •  Wane ne shi? Ayuba wani attajiri ne mai mata daya da yara kuma shi mutum mai tsoron Allah ne.

  •  Me ya sa ya so ya mutu? Farat daya munanan abubuwa suka faru da Ayuba. Ya yi rashin dukan abubuwan da yake da su. Duka yaransa sun mutu sakamakon wani bala’i. Ya kamu da cuta mai tsanani. Kuma an zarge shi da cewa shi ne ya jawo wa kansa wadannan matsalolin. Ayuba ya ce: “Ina kyamar raina, na gaji da rayuwa.”​—Ayuba 7:16.

  •  Me ya taimaka masa? Ayuba ya yi addu’a ga Allah kuma ya gaya wa mutane damuwar da yake ciki. (Ayuba 10:​1-3) Wani amininsa mai suna Elihu ya ji tausayinsa kuma ya karfafa shi. Kari ga haka, ya taimaka masa ya yi tunanin da ya dace game da yanayinsa.

  •  Ka karanta labarin Ayuba a: Ayuba 1:​1-3, 13-22; 2:7; 3:​1-13; 36:​1-7; 38:​1-3; 42:​1, 2, 10-13.

Musa

  •  Wane ne shi? Musa wani annabi mai aminci ne da ya shugabanci Isra’ilawa a zamanin dā.

  •  Me ya sa ya so ya mutu? Ayyuka sun yi wa Musa yawa kuma an yi ta masa bakar magana. Hakan ya sa Musa ya gaji sosai. Sai ya yi kuka ya gaya wa Allah cewa: “Ina rokonka ka kashe ni kawai.”​—Littafin Kidaya 11:​11, 15.

  •  Me ya taimaka masa? Musa ya gaya wa Allah yadda yake ji. Allah ya rage wa Musa yawan ayyukan da yake yi don ya sami sauki.

  •  Ka karanta labarin Musa a: Littafin Kidaya 11:​4-6, 10-17.

a Idan ka ci gaba da tunanin kashe kanka kuma ba zai yiwu ka gaya wa wani abokinka ko danginka ba, ka kira layin taimakon gaggawa idan akwai a yankinku.