Mene ne Sake Haifan Mutum Yake Nufi?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Furucin nan “haifi mutum daga bisa” (ko sake haifan mutum) yana nufin, kulla dangataka mai kyau tsakanin Allah da mutumin da aka sake haifansa. (Yohanna 3:3, 7) Allah ya fanshe su a matsayin ’ya’yansa. (Romawa 8:15, 16; Galatiyawa 4:5; 1 Yohanna 3:1) Yanayinsu yakan canja don Allah ya fanshe su su zama ’ya’yansa.—2 Korintiyawa 6:18.
Mene ne amfanin sake haifan mutum?
Yesu ya ce: “In ba a haifi mutum daga bisa ba, ba shi da iko shi ga mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:3) Idan aka sake haifan mutum, hakan yana nufin an zabe shi don ya yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Allah. A sama ne mutanen za su yi mulki, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta “sāke haifarmu” a matsayin gādon da aka ‘kebe musu a sama.’ (1 Bitrus 1:3, 4, Littafi Mai Tsarki) Wadanda aka sake haifansu sun tabbata cewa za su “yi mulki tare” Yesu Kristi.—2 Timotawus 2:12; 2 Korintiyawa 1:21, 22.
Ta yaya ake sake haifan mutum?
Sa’ad da yake tattauna wannan batun, ya ce, wanda aka sake haifansa, za a ‘haife shi daga cikin ruwa da ruhu.’ (Yohanna 3:5) Wannan furucin yana nuna cewa bayan an yi wa mutum baftisma na ruwa sai a yi masa da ruhu mai tsarki.—Ayyukan Manzanni 1:5; 2:1-4
Yesu ne mutum na farko da aka sake haifan sa. An yi masa baftisma a kogin Urdun bayan haka, aka shafe shi (ko aka yi masa baftisma) da ruhu mai tsarki. Hakan yana nufin an sake haifan Yesu da jikin ruhu da begen komawa sama ya ci gaba da rayuwa a can. (Markus 1:9-11) Allah ya ta da Yesu daga mutuwa da jikin ruhu kuma ya koma sama a matsayinsa na mala’ika don ya cika wannan nufin.—Ayyukan Manzanni 13:33.
Wadansu ma an sake haifan su bayan da aka yi musu baftisma kuma suka sami baiwar ruhu mai tsarki. * (Ayyukan Manzanni 2:38, 41) Hakan ya tabbatar musu cewa za su je sama bayan da aka ta da su daga mutuwa.—1 Korintiyawa 15:42-49.
Ra’ayin karya game da sake haifan mutum
Karya: Kafin mutum ya zama Kirista ko kuma ya sami rai na har abada sai an sake haifan sa.
Gaskiya: Ba wadanda aka sake haifan su ne kawai za su sami albarkar hadayan fansar da Yesu ya yi ba, amma har wadanda suke da begen zama a duniya. (1 Yohanna 2:1, 2; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) Mutanen da za su zauna a duniya ma Kiristoci ne, kuma za su rayu har abada.—Zabura 37:29; Matta 6:9, 10; Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.
Karya: Mutum ne zai iya ce a sake haifansa.
Gaskiya: Kowa zai iya kulla dangantaka mai kyau da Allah kuma ya sami rai na har abada. (1 Timotawus 2:3, 4; Yakub 4:8) Amma Allah ne yake zaban wadanda za a sake haifan su kuma a shafe su da ruhu mai tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinkan Allah.” (Romawa 9:16, LMT) Sake haifan mutum shi ne a “haifi mutum daga bisa” kuma hakan na nuna cewa an zabe shi ne “daga bisa” ko kuma Allah ne ya zabe shi.—John 3:3.
^ sakin layi na 9 Karniliyus da wadanda suke tare da shi ne kawai suka sami baiwar ruhu mai tsarki kafin su yi baftisma.—Ayyukan Manzanni 10:44-48.