Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah Ce?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Marubutan Littafi Mai Tsarki da yawa sun ce Allah ne ya ja-goranci abin da suka rubuta. Ka lura da waɗannan misalai:
Sarki Dauda: “Ruhun Ubangiji ya yi zance da ni, Maganatasa kuma tana bisa harshena.”—2 Samuila 23:1, 2.
Annabi Ishaya: “In ji Ubangiji, Ubangiji mai-runduna.”—Ishaya 22:15.
Manzo Yohanna: “Ru’ya ta Yesu Kristi, wanda Allah ya ba shi.”—Ru’ya ta Yohanna 1:1.