Akwai Wanda Ya Taba Ganin Allah Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Babu wani dan Adam da ya taba ganin Allah ido da ido. (Fitowa 33:20; Yohanna 1:18; 1 Yohanna 4:12) Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ruhu ne” saboda haka ’yan Adam ba za su iya ganinsa ba.—Yohanna 4:24; 1 Timotawus 1:17.
Amma mala’iku suna iya ganin Allah domin su halittun ruhu ne. (Matta 18:10) Kari ga haka, za a ta da wasu ’yan Adam da suka mutu zuwa sama kuma ta haka, za su iya ganin Allah ido da ido.—Filibiyawa 3:20, 21; 1 Yohanna 3:2.
Yadda mutum zai iya “ganin” Allah a yanzu
Littafi Mai Tsarki yakan yi amfani da kalmar nan “gani” a alamance don a nuna cewa mutum ya fahimci wani abu. (Ishaya 6:10; Irmiya 5:21; Yohanna 9:39-41) Bisa ga wannan bayanin, mutum zai iya ganin Allah a yanzu da “idanun zuciyar[sa],” wato, ta wurin kasancewa da bangaskiya da kuma fahimtar halayen Allah. (Afisawa 1:18) Littafi Mai Tsarki ya bayyana matakai da za a bi don a kasance da irin wannan bangaskiyar.
Ka koya game da halayen Allah kamar halinsa na kauna da karimci da hikima, da kuma ikonsa da ake gani ta wurin abubuwa da ya halitta. (Romawa 1:20) Bayan aka tuna wa Ayuba irin abubuwa masu ban al’ajabi da Allah ya halitta sai Ayuba ya ji kamar Allah yana dab a gabansa.—Ayuba 42:5.
Ka sami sanin Allah ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan ka bide shi [Allah], ya samu gare ka.”—1 Labarbaru 28:9; Zabura 119:2; Yohanna 17:3.
Ka koya game da Allah ta wurin rayuwar Yesu. Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban,” kuma ya fadi hakan ne domin yana kwaikwayon halin Ubansa Jehobah Allah, ciki da waje.—Yohanna 14:9.
Ka yi rayuwa a hanyar da Allah yake so kuma Allah zai yi maka albarka. Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya: gama su za su ga Allah.” Kamar yadda aka bayyana dazu, wasu da suka yi abin da Allah yake so kafin su mutu, Allah zai ta da su zuwa sama kuma za su “ga Allah.”—Matta 5:8; Zabura 11:7.
Shin Musa da Ibrahim da wasu mutane sun ga Allah ne ido da ido?
A wasu wurare a cikin Littafi Mai Tsarki inda aka ce mutane sun ga Allah ido da ido, mahallin labarin yana nuna cewa wani mala’ika ne ya wakilci Allah ko kuma ya bayyana a cikin wahayi.
Mala’iku.
A zamanin dā, Allah ya aiki mala’ikunsa a matsayin wakilai don su idar da sakonsa. (Zabura 103:20) Alal misali, akwai lokacin da Allah ya yi magana da Musa daga cikin kurmin da ke cin wuta, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Musa ya rufe fuskatasa; gama yana jin tsoro ya dubi Allah.” (Fitowa 3:4, 6) Musa bai ga Allah ido da ido ba domin mahallin ya nuna cewa “mala’ikan Allah” ne ya gani.—Fitowa 3:2.
Hakazalika, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya yi “magana da Musa fuska da fuska” hakan yana nufi ne cewa Allah ya tattauna da Musa kamar yadda abokai suke yi. (Fitowa 4:10, 11; 33:11) Musa bai gan Allah ido da ido ba domin “mala’iku” ne suka idar masa da sakon Allah. (Galatiyawa 3:19; Ayyukan Manzanni 7:53) Duk da haka, bangaskiyar Musa ta yi karfi sosai har aka ce “yana ganin wanda ba shi ganuwa.”—Ibraniyawa 11:27.
Kamar yadda Allah ya yi magana da Musa, haka ma ya yi da Ibrahim. Idan mutum ya karanta Littafi Mai Tsarki sama-sama, zai iya ganin kamar Ibrahim ya gan Allah ido da ido. (Farawa 18:1, 33) Amma mahallin ya nuna cewa Allah ya aiko ‘mutane uku’ ne su je wajen Ibrahim. Ibrahim ya fahimci cewa su wakilan Allah ne kuma ya yi magana da su kamar yana magana da Jehobah kai tsaye.—Farawa 18:2, 3, 22, 32; 19:1.
Wahayi.
Allah ya bayyana ga mutane ta wurin wahayi. Alal misali, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya ce Musa da wasu Isra’ilawa “suka ga Allah,” haka yana nufi ne cewa sun ga Allah na Isra’ila a cikin wahayi. (Fitowa 24:9-11) Hakazalika Littafi Mai Tsarki yakan ce annabawa sun “ga Ubangiji.” (Ishaya 6:1; Daniyel 7:9; Amos 9:1) A dukan wadannan aukuwar, mahallin ya nuna cewa sun gan wahayin Allah ne amma ba Shi suka gani ido da ido ba.—Ishaya 1:1; Daniyel 7:2; Amos 1:1.