Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yana da Kyau Ka Yi Ayyuka da Yawa a Lokaci Daya?

Yana da Kyau Ka Yi Ayyuka da Yawa a Lokaci Daya?

 Ka kware a yin ayyuka da yawa a lokaci daya?

 Shin ka iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya? Mutane da yawa suna gani kamar wadanda suka fara amfani da na’ura tun suna kanana sun iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya fiye da wadanda suka soma amfani da na’ura bayan da suka yi girma. Amma hakan gaskiya ne kuwa?

 KARYA ko GASKIYA?

  •   Yin abubuwa da yawa a lokaci daya zai sa ka kammala aikinka da wuri.

  •   Idan kana yin hakan a kowane lokaci za ka kware.

  •   Matasa suna iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya fiye da tsofaffi.

 Idan ka yarda da ko daya daga cikin furucin da ke sama, to, an rude ka cewa za ka iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya ke nan.

 Rudu game da yin ayyuka da yawa a lokaci daya

 Kana ganin za ka iya yin abubuwa biyu a lokaci daya? Za ka iya yin abubuwa biyu a lokaci daya idan daya daga cikin abubuwan ba ya bukatar ka mai da masa hankali sosai. Alal misali, idan kana saurarar waka yayin da kake share dakinka, watakila za ka iya yin sharan da kyau.

 Amma idan ka yi kokarin yin abubuwa biyu da kowannensu yake bukatar ka mai da masa hankali, ba za ka iya yin su biyun da kyau a lokaci daya ba. Shi ya sa wata matashiya mai suna Katherine ta ce: “Idan kana so ka wargaje kome da kake yi, to ka yi dukansu a lokaci daya.”

 Wani mai suna Caleb ya ce: “Sa’ad da nake tattauna da wani, sai aka tura mini sako ta waya da ake bukata in amsa. Na yi kokari in amsa sakon yayin da nake magana da mutumin. A sakamakon haka, ban ji yawancin abin da mutumin yake gaya mini ba, kuma na yi kuskure a kusan duka kalmomin da nake rubutawa.”

 Wata mai suna Sherry Turkle da ta yi nazarin dangantakar da ke tsakanin ’yan Adam da fasaha ta ce: “Idan muka dauka cewa muna iya yin ayyuka da yawa a lokaci daya, . . . a karshe ba za mu iya mai da hankali ga dukan abin da muke yi yadda ya kamata ba. Yin abubuwa da yawa a lokaci daya yana iya sa mu dauka cewa muna yin ayyuka da kyau, alhali kuskure muke tabkawa.” *

 Wata mai suna Tamara ta ce: “A wasu lokuta, nakan yi zato cewa zan iya tattaunawa da mutum yayin da nake tura sako a wayata. Amma sai na ga cewa abin da ya kamata in rubuta a sakon ne na furta kuma abin da ya kamata in furta ne na rubuta a sakon!”

 Mutanen da suke kokarin yin ayyuka da yawa a lokaci daya suna ba kansu wahala ne kawai. Alal misali, yana daukan su dogon lokaci kafin su gama aikin makaranta. Ko su kasa yin aikin makarantar da kyau kuma su bukaci sake yin sa. Ko da aiki ya dauke su dogon lokaci ne ko kuma sun kasa yin sa da kyau, a karshe, masu yin ayyuka da yawa a lokaci daya ba sa samun isashen lokaci!

 Wani likitan kwakwalwa mai suna Thomas Kersting ya ce idan mutum ya yi kokarin yin ayyuka da yawa sosai a lokaci daya, kwakwalwarsa takan rikice. *

 Wata mai suna Teresa ta ce: “Idan ka yi kokarin yin ayyuka da yawa a lokaci daya, ba za ka mai da hankali ga wasu bayanai masu muhimmanci ba. A karshe, za ka dada wa kanka aiki ne kawai kuma ka bata wa kanka lokaci.”

Yin ayyuka da yawa a lokaci daya yana kama da kokarin yin tuki a kan hanyoyi biyu a lokaci daya

 Hanya mafi kyau na yin ayyuka

  •   Ka koyi yadda za ka rika mai da hankali ga yin abu daya a lokaci daya. Hakan yana iya yi maka wuya, musamman idan ka saba yin abubuwa da yawa a lokaci daya, kamar tura sako ta waya yayin da kake yin nazari. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zaɓi abubuwa mafifita.” (Filibiyawa 1:​10, Littafi Mai Tsarki) Ba dukan abubuwan da muke yi ba ne suke da muhimmanci. Don haka, ka zabi wanda ya fi muhimmanci kuma ka mai da hankali ga yin sa har sai ka gama.

     Wata mai suna Maria ta ce: “Kwakwalwarka tana kama da karamin yaro da yake son yin duk abin da ya ga dama, amma dole ne a wasu lokuta ka hana shi, duk da cewa zai fi sauki ka bar shi ya yi abin da yake so.”

  •   Ka kawar da duk wani abin da zai raba hankalinka. Shin kana ji kamar ka rika wasa da wayarka sa’ad da kake yin nazari? Ka ajiye ta a wani wuri nesa da kai. Ka kashe talabijin kuma kada ka ma yi tunanin shiga dandalin sada zumunta! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kuna amfani da kowane zarafin da kuke da shi” da kyau.​—Kolosiyawa 4:5.

     Wata mai suna Onya ta ce: “Na gano cewa yin abu daya a lokaci daya ya fi amfana ta. Hakan yana sa ni farin ciki sa’ad da na kammala daya daga cikin abubuwan da nake so in yi. Hakan yana sa in samu gamsuwa.”

  •   Sa’ad da kake tattaunawa da wani kada ka bari wani abu ya raba hankalinka. Idan kana danna wayarka sa’ad da kake tattaunawa da wani, hakan rashin kunya ne kuma zai iya bata tattaunawar. Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi wa mutane abin da muke so su yi mana.​—Matiyu 7:12.

     Wani mai suna David ya ce: “A wasu lokuta sa’ad da nake tattaunawa da ’yar’uwata, sai ta rika tura sako da wayarta ko kuma ta rika yin wasa da wayar. Hakan yana bata mini rai! Amma gaskiyar ita ce, ni ma ina yin hakan a wasu lokuta!”

^ Daga littafin nan Reclaiming Conversation.

^ Daga littafin nan Disconnected.