Koma ka ga abin da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | JONATHAN

Sun Kulla Abota ta Kwarai

Sun Kulla Abota ta Kwarai

An gama yakin kuma ko’ina a Kwarin Elah ya yi shuru. Yayin da iska take kada bukkokin da sojojin suka kafa, Sarki Shawulu ya kira wasu daga cikin sojojinsa don su yi magana. Dan farinsa, Jonathan yana cikinsu, kuma wani matashi makiyayi yana ba su labarin kansa. Dauda ne matashin, kuma yana magana da karfin zuciya da kuma himma. Shawulu ya kasa kunne sosai don ya ji labarin da Dauda yake bayarwa da kyau. Yaya Jonathan ya ji da ya ga hakan? Ya dade yana cin nasara a yakin da suke yi da makiyan Jehobah. Amma a wannan karon, matashin ne ya taimaka aka sami nasara, ba Jonathan ba. Dauda ya kashe Goliyat! Shin daukakar da Dauda ya samu ya sa Jonathan kishi ne?

Abin da Jonathan ya yi zai iya ba ka mamaki. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Bayan da Dauda ya gama magana da Shawulu, sai Jonathan dan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dauda sosai. Jonathan kuwa ya kaunaci Dauda kamar ransa.’ Jonathan ya ba wa Dauda kayan yakinsa har da bakansa. Wannan ba karamin abu ba ne domin Jonathan kwararen maharbi ne. Kari ga haka, Jonathan da Dauda sun yi wa juna alkawari cewa za su taimaka wa juna kuma za su zama abokai na din-din-din.​—1 Sama’ila 18:​1-5.

Da haka suka zama abokai kuma abotarsu tana ciki abota mafi kyau da ke Littafi Mai Tsarki. Masu bangaskiya ba sa wasa da abotarsu. Idan muka zabi abokan kirki, kuma mu da kanmu muka zama abokan kirki, za mu taimaka wa juna mu dada kasancewa da bangaskiya a wannan mugun zamanin da muke ciki. (Karin Magana 27:17) Yanzu bari mu ga abin da Jonathan ya koya mana game da abokantaka.

Abin da Ke Sa Abota Ta Yi Danko

Ya aka yi suka zama abokai da wuri haka? Abin da ya sa suka zama abokai ne ya sa hakan ya yiwu. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka faru kafin lokacin. Jonathan yana fama da wasu matsaloli. Halin babansa, wato Sarki Shawulu yana dada muni kowace rana. A dā shi mai saukin kai ne, mai tsoron Allah, amma yanzu ya zama mai girman kai da rashin biyayya ga Allah.​—1 Sama’ila 15:​17-19, 26.

Babu shakka mugun halin babansa ya dame Jonathan sosai domin Jonathan yana kaunar babansa. (1 Sama’ila 20:2) Watakila Jonathan ya damu da yadda halin babansa zai iya shafan al’ummar Isra’ila gaba daya. Da yake babansa ne sarki, Jonathan bai so rashin biyayyarsa ya sa Jehobah ya yi watsi da mutanen kasar ba. Jonathan mai bangaskiya ne sosai, don haka wannan yanayin bai zama masa da sauki ba.

Watakila wannan yanayin ne ya sa Jonathan ya kulla abota da Dauda. Jonathan ya ga cewa Dauda mai bangaskiya ne sosai. Ka tuna cewa, Dauda ba kamar sojojin Shawulu ba ne da suka gagara tinkarar wani katon mutum mai suna Goliyat. Dauda ya yi imani cewa da taimakon Jehobah, zai fi karfin Goliyat, duk da cewa Goliyat yana da kayan yaki.​—1 Sama’ila 17:​45-47.

Shekaru kafin haka, Jonathan ma ya nuna irin karfin halin nan. Ya yi imani cewa shi da mai rike masa kayan yaki za su iya yakan tarin sojojin da ke da kayan yaki sosai. Me ya ba shi wannan kafin halin? Jonathan ya ce: “Babu abin da zai iya hana Yahweh kawo nasara.” (1 Sama’ila 14:6) Hakika, Jonathan da Dauda masu bangaskiya ne kuma suna kaunar Jehobah sosai. Abin da ya sa mutane biyun nan suka kulla abota mai danko ke nan. Jonathan yarima ne kuma shi jarumi ne mai shekara kusan 50, Dauda kuma makiyayi ne da watakila bai kai shekara 20 ba. Duk da haka, Jonathan bai damu da bambancin da ke tsakaninsu ba. *

Alkawarin da suka yi wa juna ya kāre dangantakarsu. Me ya sa muka ce haka? Domin Dauda ya riga ya san cewa shi ne Jehobah ya zaba ya zama sarkin Isra’ila bayan Shawulu! Amma, ya ki ya gaya wa Jonathan ne? Ko kadan! A ce suna boye-boye ko suna yi wa juna karya, da ba su zama abokai na kud-da-kud haka ba. Da Jonathan ya ji cewa Dauda ne zai zama sarki, me ya yi? A ce Jonathan yana sa ran zama sarki don ya daidaita munanan abubuwan da babansa ya yi fa? Littafi Mai Tsarki bai ce Jonathan ya ji wani iri sa’ad da ya ji wannan labarin ba; ya dai gaya mana yadda Jonathan ya kasance da aminci da bangaskiya, kuma abin da ya fi muhimmanci ke nan. Jonathan ya ga cewa ruhun Jehobah yana tare da Dauda. (1 Sama’ila 16:​1, 11-13) Don haka, Jonathan ya cika alkawarin da ya yi, kuma ya ci gaba da daukan Dauda a matsayin amininsa, ba abokin gāba ba. Nufin Jehobah ne Jonathan yake so ya cika.

Jonathan da Dauda masu bangaskiya ne kuma suna kaunar Jehobah sosai

Wannan abokantakar ta amfane su biyun sosai. Me muka koya daga yadda Jonathan ya nuna bangaskiya? Ya kamata bayin Allah su dauki abokansu da muhimmanci sosai. Ba sai mun yi abokantaka da tsaranmu ko wadanda matsayinmu daya da su ba. Muddin abokanmu suna tsoron Allah, za su karfafa mu sosai. Jonathan da Dauda sun karfafa juna sau da yawa. Kuma abin da ya faru daga baya, ya sa sun bukaci su taimaka wa juna sosai.

Wa Zai Manne Wa?

Da farko, Shawulu ya kaunaci Dauda, har ya sa ya zama kwamandan sojojinsa. Amma ba da dadewa ba, Shawulu ya soma kishin Dauda, abin da Jonathan ya ki yi. Dauda ya yi ta yin nasara a kan Filistiyawa wadanda magabtan Isra’ila ne. Hakan ya sa mutane sun so shi kuma sun yi ta yaba masa. Har wasu mata a Isra’ila sun rera waka suna cewa: ‘Shawulu ya kashe dubbai, Dauda dubun dubbai.’ Wakar ta bata wa Shawulu rai sosai. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Daga ranar nan Shawulu ya sa wa Dauda ido domin yana kishinsa.’ (1 Sama’ila 18:​7, 9) Yana ganin kamar Dauda zai kwace sarauta daga wurin shi. Amma Shawulu ya yi wauta. Ko da yake Dauda ya san cewa shi ne zai yi sarauta bayan Shawulu, bai taba tunanin yi masa juyin mulki ba don ya san cewa Jehobah ne ya nada Shawulu.

Shawulu ya kulla makirci don a kashe Dauda a yaki, amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba. Dauda ya yi ta samun nasara a yaki kuma mutane sun daraja shi sosai. Daga baya, Shawulu ya gaya wa bayinsa da dansa Jonathan cewa yana so ya kashe Dauda don su goyi bayansa. Babu shakka halin babansa ya sa Jonathan bakin ciki sosai. (1 Sama’ila 18:​25-30; 19:1) Jonathan mai aminci ne ga babansa, amma ya kasance da aminci ga abokinsa ma. Yanzu da ya zama masa dole ya goyi bayan dayansu, ga wa zai manne?

Jonathan ya gaya wa babansa cewa: ‘Ranka ya dade! Kada ka yi wa bawanka Dauda wani laifi. Bai taba yi maka laifi ba, a maimakon haka dukan abubuwan da ya yi sun zama da taimako zuwa gare ka sosai. Ya sadaukar da ransa lokacin da ya kashe Goliyat. Ranar nan Yahweh ya kawo babban ceto ga dukan Isra’ila. Kai ma da ka ga wannan ka yi murna. To, don me yanzu kake so ka yi wa mai aminci laifi? Kada ka kashe Dauda babu dalili!’ Shawulu ya yi kamar ya aminci da abin da Jonathan ya gaya masa, har ya dau alkawari cewa ba zai kashe Dauda ba. Amma Shawulu bai cika alkawarinsa ba. Da ya ga cewa Dauda ya ci gaba da samun nasara, haushi ya kama shi sosai har ya jefi Dauda da kibiya! (1 Sama’ila 19:​4-6, 9, 10) Amma Dauda ya kauce masa kuma ya gudu daga fadar Shawulu.

Ka taba kasancewa a yanayin da ka rasa wanda za ka manne wa? Hakan ba dadi sam. A irin yanayin nan, wasu mutane za su iya ba ka shawara cewa bin ra’ayin danginka ne ya fi muhimmanci. Amma Jonathan ya san cewa bin ra’ayin babansa a wannan lokacin ba daidai ba ne, domin Dauda bawan Allah mai aminci ne. Jonathan ya zabi ya kasance da aminci ga Jehobah. Shi ya sa ya goyi bayan Dauda. Ko da yake amincinsa ga Jehobah ne ya fi masa muhimmanci, Jonathan bai yi watsi da babansa ba. Ya ba shi shawarar da ta dace maimakon ya yi masa zakin baki. Mu ma za mu amfana idan muka kasance da aminci kamar Jonathan.

Abin da Ya Biyo Baya don Amincinsa

Jonathan ya sake kokarin taimaka wa Shawulu ya sasanta da Dauda, amma Shawulu ya ki jin sa. Ana nan, sai Dauda ya zo a boye kuma ya gaya wa Jonathan cewa ransa na cikin hadari. Dauda ya gaya wa abokinsa cewa: “Ina gab da mutuwa.” Jonathan ya ce masa zai gwada babansa ya ga ko za su sulhunta, sa’an nan zai gaya wa Dauda sakamakon hakan. Ya ce Dauda ya boye, sa’an nan zai gaya masa abin da ake ciki ta wurin amfani da kwari da baka. Jonathan ya gaya masa cewa: “Ka ci gaba da nuna wa iyalina kaunarka marar canjawa har abada. Bari Yahweh ya halaka abokan gābanka daga fuskar duniya.” Kuma ya sa Dauda ya yi alkawari cewa zai yi hakan. Dauda ya yarda cewa zai kula da ’yan gidan Jonathan kuma zai kāre su.​—1 Sama’ila 20:​3, 13-27.

Jonathan ya yi kokari ya yi magana mai kyau game da Dauda a gaban Shawulu, amma sarkin ya yi fushi sosai! Ya gaya wa Jonathan cewa: “Kai shege ne kuma haifuwar banzan mace.” Ya kuma ce amincinsa ga Dauda abin kunya ne ga iyalinsu. Ya yi kokari ya sa Jonathan ya yi tunanin kansa, ya ce: ‘Muddin dan Jesse yana da rai a duniya ba za ka yi mulki ba, kuma ba za ka iya tabbatar da lafiyar ranka ba.’ Jonathan bai canja ra’ayinsa ba, kuma ya sake rokon babansa ya ce: “Don me za a kashe shi? Mene ne ya yi?” Sai Shawulu ya kai wa Jonathan hari! Ko da yake Shawulu ya tsufa, har ila shi kwararren mayaki ne. Ya jefi dansa da kibiya! Amma duk da kwarewarsa, bai same shi ba. Abin da ya faru ya bata wa Jonathan rai sosai kuma ya ji kunya, sai ya tashi ya bar wurin.​—1 Sama’ila 20:​24-34.

Jonathan bai bar son kai ya hana shi yin abin da ya dace ba

Washegari, Jonathan ya je kusa da wurin da Dauda ya buya. Kuma kamar yadda suka shirya, Jonathan ya harba kibiya don ya nuna cewa har ila Shawulu yana so ya kashe Dauda. Sai Jonathan ya ce wa bawansa ya koma gida shi kuma ya je ya sami Dauda. Da yake su biyu ne kawai suka rage, sun sami damar yin magana na dan lokaci. Su biyun sun yi kuka kuma suka yi ban kwana da juna. Daga nan sai Dauda ya tafi kuma ya zama dan gudun hijira.​—1 Sama’ila 20:​35-42.

Jonathan ya nuna cewa shi mai aminci ne ba mai son kai ba duk da matsalolin da suke kasa. Shaidan makiyin dukan mutane masu aminci ne, don haka, zai fi so ya ga Jonathan ya bi ra’ayin babansa na son iko da matsayi fiye da kome. Shaidan yana so ya dinga sa mutane su zama masu son zuciya. Abin da ya yi da iyayenmu na farko Adamu da Hauwa’u ke nan kuma ya yi nasara. (Farawa 3:​1-6) Amma ya gagara rudin Jonathan. Babu shakka, hakan ya bata wa Shaidan rai sosai! Shin, za ka tsallake tarkonsa? A zamaninmu, masu son kansu sun yi yawa a duniya. (2 Timoti 3:​1-5) Zai yiwu mu zama masu aminci, da kuma marasa son kai kamar Jonathan kuwa?

Jonathan ya nuna wa abokinsa cewa yana cikin hadari ta wajen harba kibiya, domin shi abokin kirki ne

“Kaunatacce Kake a Gare Ni”

A kwana a tashi, Shawulu ya dada tsanan Dauda. Jonathan ya ga yadda babansa ya soma yi kamar wanda ya fita daga hayyacinsa, ya tara sojojinsa suna zagaya kasar gaba daya suna neman su kashe mutum daya marar laifi. Kuma Jonathan ya kasa yin kome. (1 Sama’ila 24:​1, 2, 12-15; 26:20) Jonathan ya bi su ne? Babu inda aka rubuta a Littafi Mai Tsarki cewa Jonathan ya bi su. Jonathan bai yi hakan ba domin ya rike amincinsa ga Jehobah da Dauda kuma ya mutunta alkawarin da shi da Dauda suka yi wa juna.

Bai daina kaunar abokinsa ba. Da shigewar lokaci, ya yi kokari ya sake haduwa da Dauda kuma sun hadu a Horesh. Ma’anar Horesh shi ne, “Wurin Itatuwa.” Horesh yana wani daji da ke yanki mai tuddai, kuma watakila bai da nisa sosai daga kudu maso gabashin Hebron. Me ya sa Jonathan ya jefa ransa cikin hadari don ya je ya ga wannan dan gudun hijira? Littafi Mai Tsarki ya ce ya yi hakan ne don ya karfafa Dauda “ya tsaya ga Allah,” wato, ya dogara ga Jehobah. (1 Sama’ila 23:16) Mene ne Jonathan ya gaya masa?

Jonathan ya gaya wa abokinsa cewa, “kada ka ji tsoro.” Ya kuma tabbatar masa cewa, “babana Shawulu ba zai iya yi maka kome ba.” Me ya ba shi karfin zuciya haka? Jonathan ya yi imani cewa duk abin da Jehobah ya fada ba shakka zai faru. Sa’an na ya ce masa, “kai ne za ka zama sarkin Isra’ila.” Abin da Jehobah ya umurci annabi Sama’ila ya fada game da Dauda ke nan shekaru kafin wannan lokacin. A wannan karon, Jonathan ya sake tuna wa Dauda cewa a kullum Jehobah yana cika alkawarin da ya yi. Wani matsayi ne Jonathan yake ganin zai samu? Ya ce: “Ni kuma zan zama na biye da kai.” Hakika, Jonathan ya nuna saukin kai sosai! Ya amince ya zama a karkashin Dauda kuma ya goyi bayansa, ko da yake ya girme shi da wajen shekara 30. Jonathan ya kammala da cewa: “Babana Shawulu ma ya san da haka.” (1 Sama’ila 23:​17, 18) A ra’ayinsa, babansa ya riga ya san cewa ba zai yi nasara a kan mutumin da Jehobah ya riga ya zaba ya zama sarki bayan shi ba!

Jonathan ya karfafa Dauda sa’ad da yake bukatar hakan

Babu shakka, Dauda ya dade yana tuna abubuwan da suka yi magana a kai a lokacin da suka hadu. Ba su sake ganin juna bayan wannan lokacin ba. Abin bakin ciki shi ne, Jonathan bai samu damar zama na biyun Dauda ba.

Jonathan ya bi mahaifinsa zuwa yaki da Filistiyawa, makiyan al’umar Isra’ila. Ya bi mahaifinsa yakin nan da zuciya daya domin hidimar Jehobah ce ta fi muhimmanci a gare shi. Bai bar kurakuran babansa su hana shi ba. Ya yi amfani da basirarsa da karfinsa a yakin kamar yadda ya saba, duk da haka, Isra’ilawa ba su yi nasara ba. Shawulu ya ci gaba da yi wa Allah rashin biyayya har ya saka hannu a sihiri, kuma Dokar Jehobah ta ce ya kamata a kashe duk wanda ya yi hakan. Don haka Jehobah ya daina taimaka wa Shawulu. A yakin, an kashe ’ya’yan Shawulu guda uku, har da Jonathan. An ji wa Shawulu rauni sosai, sai ya kashe kansa.​—1 Sama’ila 28:​6-14; 31:​2-6.

Jonathan ya ce: “Za ka zama sarkin Isra’ila, ni kuma zan zama na biye da kai.”​—1 Sama’ila 23:17

Hakan ya sa Dauda bakin ciki sosai. Dauda ya yi makoki domin Shawulu duk da muguntar da ya yi masa, domin Dauda mai alheri ne kuma yana gafartawa. Dauda ya rubuta wata wakar makoki game da Shawulu da Jonathan. Kuma mai yiwuwa abin da Dauda ya fada game da babban abokinsa a wakar ne ya fi ratsa zuciya, ya ce: ‘Na yi bakin ciki sosai saboda kai, dan’uwana Jonathan, kaunatacce kake a gare ni. Kaunarka gare ni ba misali, ta fi kaunar mace da namiji.’​—2 Sama’ila 1:26.

Dauda ya cika alkawarin da ya yi wa Jonathan. Shekaru bayan haka, ya nemi Mefiboshet dan Jonathan, wanda gurgu ne, kuma ya kula da shi. (2 Sama’ila 9:​1-13) Hakika, Dauda ya koyi halaye masu kyau daga wurin Jonathan. Jonathan mai aminci da kuma saukin kai ne, kuma ya manne wa abokinsa duk da cewa hakan bai zama masa da sauki ba. Shin, mu ma za mu iya koyan wadannan halayen? Za mu iya neman abokan da suke da halaye kamar Jonathan? Ta yaya mu kanmu za mu zama abokan kirki kamar Jonathan? Za mu iya yin hakan idan muna taimaka wa abokanmu su kusaci Jehobah, muka sa ibadarmu a kan gaba, kuma muka nuna wa abokanmu aminci ba tare da son kai ba. Ta hakan za mu yi koyi da bangaskiyar Jonathan.

^ sakin layi na 7 A lokacin da babansa ya soma mulki ne aka fara ambata sunan Jonathan a cikin Littafi Mai Tsarki, a matsayin kwamandan sojoji. Hakan ya nuna cewa ya kai shekara 20. (Littafin Kidaya 1:3; 1 Sama’ila 13:2) Shawulu ya yi shekara 40 yana mulki. Don haka, Jonathan ya kai wajen shekara 60 sa’ad da Shawulu ya mutu. Dauda yana dan shekara 30 Shawulu ya mutu. (1 Sama’ila 31:2; 2 Sama’ila 5:4) Hakan ya nuna cewa Jonathan ya girme Dauda da wajen shekara 30.