WAƘA TA 68
Mu Taimaki Mutane Su Bauta wa Jehobah
(Matta 13:4-8)
-
1. Mu yi aikin Ubangijinmu,
Mu riƙa bin dokokinsa.
Ubangiji ne ja-goranmu,
Zai koya mana hanyarsa.
Idan muna wa’azin bishara
Wasu za su saurare mu.
Don hakan mu yi iya ƙoƙarinmu
Kuma mu yi wa’azi sosai.
-
2. In muna yin shela da himma
Za mu iya yin nasara.
Za mu taimaka wa mutane
Domin su bauta wa Allah.
Mu kawar da shakkar da suke yi
Domin su iya jimrewa.
Za mu yi murna sosai idan mun ga
Yadda suke samun ci gaba.
(Ka kuma duba Mat. 13:19-23; 22:37.)