WAƘA TA 47
Mu Rika Addu’a ga Jehobah Koyaushe
(1 Tasalonikawa 5:17)
-
1. Mu riƙa addu’a ga Jehobah.
Ya ba mu gatan zama shaidunsa.
Mu gaya masa duk damuwarmu,
Mu dogara gare shi a kullum.
Mu yi addu’a kullum.
-
2. Mu yi godiya don muna da rai,
Mu roƙe shi ya gafarta mana.
Mu gaya wa Allah kasawarmu.
Allahnmu ya san mu ajizai ne.
Mu yi addu’a kullum.
-
3. Mu roƙe shi lokacin wahala,
Shi Ubanmu ne da amininmu.
Za ya kāre mu, ya taimake mu,
Kar mu ji tsoro, zai kula da mu.
Mu yi addu’a kullum.
(Ka kuma duba Zab. 65:5; Mat. 6:9-13; 26:41; Luk. 18:1.)