Privacy Settings

To provide you with the best possible experience, we use cookies and similar technologies. Some cookies are necessary to make our website work and cannot be refused. You can accept or decline the use of additional cookies, which we use only to improve your experience. None of this data will ever be sold or used for marketing. To learn more, read the Global Policy on Use of Cookies and Similar Technologies. You can customize your settings at any time by going to Privacy Settings.

Shawara a Kan Yin Bincike

Shawara a Kan Yin Bincike

Abubuwan Yin Bincike a Watchtower LABURARE NA INTANE

Muna da abubuwan yin bincike da za su taimaka maka ka bincika abubuwa da yawa. A cikinsu, akwai Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah, da Glossary, da Insight on the Scriptures, da kuma Watch Tower Publications Index. Kuma dukansu suna cikin Watchtower LABURARE NA INTANE.

Sashen yin bincike da ke Watchtower LABURARE NA INTANE zai taimaka maka ka yi amfani da abubuwan nan da kyau. Idan ka rubuta abu a inda aka ce “Rubuta Batu,” za ka ga batutuwa dabam-dabam sun bayyana a ƙarƙashinsa. A cikin abubuwa da za a jero maka, za ka ga kalmar nan “Batu” a gefen wanda yake cikin abubuwan bincike da muka ambata.

Ka gwada yi: Ka fara da rubuta kalmar nan “Jehobah” a inda aka ce “Rubuta Batu” (A). A cikin batutuwa da aka jero maka, ka zaɓi wanda aka rubuta da ke da kalmar nan “Batu” a gefensa (B). Za ka ga abubuwa da aka rubuta game da batun da aka ɗauko daga abubuwan bincikenmu da ma wasu wurare.

Sashen yin bincike da ke “Watchtower LABURARE NA INTANE.” Alamar A tana nuna kalmar da aka rubuta a cikin sashen binciken. Alamar B tana nuna kalmar nan “Batu” a gefen abubuwan da aka jera.