Mu Na Jehobah Ne
“Mai albarka ce al’ummar da Yahweh shi ne Allahnta, jama’ar da ya zaɓa su zama gādonsa!”—ZAB. 33:12.
1. Me ya sa muka ce kome na Jehobah ne? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
KOME na Jehobah ne! Shi ne ya halicci “saman sammai, da duniya, da dukan abubuwan da suke cikinta.” (M. Sha 10:14; R. Yar. 4:11) Da yake Jehobah ne ya halicci kome, dukanmu na shi ne. (Zab. 100:3) Amma a cikin dukan mutanen da suka yi rayuwa a duniyar nan, Jehobah ya zaɓi wasu su zama bayinsa na musamman.
2. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, su waye ne jama’ar Allah ta musamman?
2 Alal misali, littafin Zabura 135 ya ce bayin Jehobah a ƙasar Isra’ila ta dā “abinsa mai daraja” ne. (Zab. 135:4) Ƙari ga haka, littafin Hosea ya annabta cewa wasu da ba Isra’ilawa ba ne za su zama bayin Jehobah. (Hos. 2:23) Annabcin ya cika sa’ad da Jehobah ya soma zaɓar mutanen da ba Isra’ilawa ba su yi sarauta da Yesu. (A. M. 10:45; Rom. 9:23-26) Wannan ‘al’umma mai tsarki’ “jama’ar Allah ta musamman” ce. Allah ya shafe su da ruhunsa mai tsarki kuma ya zaɓe su su yi rayuwa a sama. (1 Bit. 2:9, 10) Amma sauran Kiristoci fa da suke da begen yin rayuwa a duniya? Jehobah ya kira su “mutanena” da kuma “mutanena da na zaɓa.”—Isha. 65:22.
3. (a) Su waye ne a yau suke da dangantaka ta musamman da Jehobah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
Luk. 12:32; Yoh. 10:16) Ya kamata mu nuna wa Jehobah cewa muna godiya sosai don yadda ya ba mu gatan zama abokansa. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi da yawa da za mu iya nuna godiya ga Jehobah don wannan gata da ya ba mu.
3 A yau, “ƙaramin garke” masu begen yin rayuwa a sama da kuma “waɗansu tumaki” masu begen yin rayuwa a duniya “garke ɗaya” ne da Jehobah ke ɗauka a matsayin mutanensa. (MUN YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH
4. Ta yaya za mu iya yin godiya ga Jehobah don ya ba mu zarafin ƙulla dangantaka da shi, kuma ta yaya Yesu ya yi hakan?
4 Muna nuna godiya ga Jehobah ta wajen yin alkawarin bauta masa da kuma yin baftisma. Sa’ad da muka yi baftisma, muna nuna wa kowa cewa mun zama na Jehobah kuma muna a shirye mu bi dokokinsa. (Ibran. 12:9) Abin da Yesu ya yi ke nan a lokacin da ya yi baftisma. Ya ce wa Jehobah: “Ina marmari in aikata nufinka, ya Allahna.” (Zab. 40:7, 8) Yesu ya ba da kansa ga yin nufin Jehobah ko da yake an haife shi cikin al’ummar da ta riga ta yi alkawarin bauta wa Allah.
5, 6. (a) Yaya Jehobah ya ji sa’ad da Yesu ya yi baftisma? (b) Ka ba da misalin da ya nuna cewa Jehobah yana murna sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa shi kaɗai.
5 Yaya Jehobah ya ji sa’ad da Yesu ya yi baftisma? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da aka yi wa Yesu baftisma, ya fito daga ruwan ke nan, sai ga ruhun Allah yana saukowa a kamannin kurciya, har ya sauka a kansa. Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, ‘Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa ƙwarai.’ ” (Mat. 3:16, 17) Ko da yake Yesu na Jehobah ne tun asali, amma Jehobah ya yi murna cewa Yesu yana a shirye ya yi nufinsa kaɗai. Hakazalika, Jehobah yana murna sa’ad da muka yi alkawarin bauta masa kuma zai albarkace mu.—Zab. 149:4.
6 Alal misali, a ce ka shuka masara a gonarka. Sai wata rana, ’yarka ƙarama ta karya masara guda ta ba ka. Yaya za ka ji? Gaskiya ne cewa masarar ta ka ce tun asali, amma da yake kai uba ne mai ƙauna, ba za ka yi irin wannan tunanin ba. A maimakon haka, za ka yi farin cikin karɓan masarar don hakan ya nuna cewa ’yarka tana ƙaunarka sosai. Babu shakka, za ka daraja masarar fiye da sauran da ke gonar. Haka Jehobah yake murna sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa shi kaɗai.—Fit. 34:14.
7. Ta yaya Malakai ya nuna yadda Jehobah yake ɗaukan mutanen da suke bauta masa da yardar rai?
7 Karanta Malakai 3:16. Me ya sa yake da muhimmanci ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma? Gaskiya ne cewa tun lokacin da aka haifi dukanmu, mu na Jehobah ne. Amma ka yi tunanin irin murnar da Jehobah zai yi idan ka nuna cewa ka amince da shi a matsayin Allah Maɗaukaki ta wajen yin alkawarin bauta masa. (K. Mag 23:15) Jehobah ya san mutanen da suke bauta masa da dukan zuciyarsu kuma yana rubuta sunayensu a “littafin tunawa.”
8, 9. Mene ne Jehobah yake bukata daga mutanen da aka rubuta sunayensu a “littafin tunawa”?
8 Da akwai abubuwan da muke bukatar mu yi don a rubuta sunayenmu a “littafin tunawa.” Malakai ya ce dole ne mu riƙa ‘tsoron Yahweh’ kuma mu yi ‘tunanin Fit. 32:33; Zab. 69:28.
sunansa.’ Idan muna bauta wa wani abu ko kuma wata halitta dabam, hakan zai sa Jehobah ya soke sunayenmu daga littafin rai.—9 Saboda haka, ba yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma kaɗai muke bukatar mu yi ba. Waɗannan abubuwa ne da muke yi sau ɗaya kawai. Amma bauta wa Jehobah abu ne da muke bukatar mu ci gaba da yi. A kowace rana, muna bukatar mu riƙa nunawa ta ayyukanmu cewa muna biyayya ga Jehobah.—1 Bit. 4:1, 2.
MU GUJE WA SHA’AWOYIN BANZA
10. Wane bambanci ne ya kamata a gani tsakanin masu bauta wa Jehobah da waɗanda ba sa bauta masa?
10 A talifi na baya, mun tattauna labarin Kayinu da Sulemanu da kuma Isra’ilawa. Dukansu sun yi da’awar bauta wa Jehobah, amma ba su yi hakan da zuciya ɗaya ba. Waɗannan misalan sun nuna sarai cewa wajibi ne dukan bayin Jehobah su goyi bayansa kuma su nisanta kansu daga munanan ayyuka. (Rom. 12:9) Shi ya sa bayan Malakai ya ambata “littafin tunawa,” Jehobah ya yi magana game da “bambanci tsakanin mai adalci da mugu, kuma tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.”—Mal. 3:18.
11. Me ya sa ya kamata ya kasance a bayyane ga kowa cewa mu bayin Jehobah ne?
11 Ga wata hanya kuma da za mu iya nuna godiya ga Jehobah don ya zaɓe mu a matsayin mutanensa. Ya kamata ya kasance a bayyane ga kowa cewa mu bayin Jehobah ne. (1 Tim. 4:15; Mat. 5:16) Ka yi wa kanka waɗannan tambayoyin: ‘Mutane suna gani cewa ina da aminci ga Jehobah? Ina alfaharin gaya wa mutane cewa ni Mashaidin Jehobah ne ko kuma Mashaidiyar Jehobah ce?’ Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya zaɓe mu a matsayin mutanensa. Saboda haka, idan mun ƙi sa mutane su san cewa mu bayinsa ne, hakan zai sa shi baƙin ciki sosai.—Zab. 119:46; karanta Markus 8:38.
12, 13. Ta yaya wasu suke sa ya kasance da wuya a san su a matsayin Shaidun Jehobah?
12 Abin baƙin ciki ne cewa wasu Shaidun 1 Kor. 2:12) Ruhun duniya ne yake sa mutane ‘bin sha’awace-sha’awacen jikinsu.’ (Afis. 2:3) Alal misali, duk da cewa ƙungiyar Jehobah ta yi gargaɗi sau da yawa game da irin kayan da ya kamata mu riƙa sakawa da kuma adon ya dace mu riƙa yi, wasu suna yin abin da suka ga dama. Suna saka kaya masu matse jikinsu da kuma waɗanda ke sa a ga siffar jikinsu. Suna ma saka su zuwa taron ikilisiya da manyan taro. Wasu suna yin askin da bai dace ba ko kuma kitso ko irin sumar da ba ta dace ba. (1 Tim. 2:9, 10) A sakamakon haka, idan suna cikin jama’a, yana kasancewa da wuya a san ko su bayin Jehobah ne ko kuma ‘abokan duniya.’—Yaƙ. 4:4.
Jehobah ba sa barin mutane su ga bambanci “tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa,” domin suna yin koyi da “ruhun duniya.” (13 Da akwai wasu hanyoyi kuma da wasu Shaidu suke yin koyi da mutanen duniya. Alal misali, idan ana yin biki ko liyafa, suna yin rawa da kuma abubuwan da ba su dace da Kiristoci ba. Suna saka hotunansu da ba su dace ba a dandalin sada zumunta na intane kuma suna yin kalaman da ba su dace da Kiristoci ba. Wataƙila ba a taɓa musu horo a ikilisiya ba a sakamakon yin zunubi mai tsanani, amma suna ɓata mutanen da suke neman su yi koyi da misalai masu kyau na bayin Jehobah.—Karanta 1 Bitrus 2:11, 12.
14. Me ya kamata mu yi don mu kāre dangantakarmu da Jehobah?
14 Duniyar nan tana matsa mana mu mai da hankali ga “sha’awa ta jiki, da kwaɗayin ido, da kuma taƙama da abubuwan rayuwa.” (1 Yoh. 2:16) Amma da yake mu bayin Jehobah ne, Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa mu “bar rayuwa marar halin Allah, da sha’awace-sha’awacen duniya, mu kame kanmu, mu zama masu gaskiya a zuci, muna masu halin Allah a wannan duniya.” (Tit. 2:12) Ya kamata salon rayuwarmu gabaki ɗaya, wato furucinmu da yadda muke ci da sha da adonmu da kayan da muke sakawa da kuma aikinmu su nuna wa mutane sarai cewa mu bayin Jehobah kaɗai ne.—Karanta 1 Korintiyawa 10:31, 32.
MUNA NUNA WA ‘JUNA ƘAUNA TA AINIHI’
15. Me ya sa ya dace mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu da kuma kyautata musu?
15 Muna nuna cewa mun daraja abotarmu da Jehobah ta yadda muke bi da ’yan’uwanmu Kiristoci. Su ma bayin Jehobah ne. Idan muna tunawa da hakan, za mu riƙa nuna musu ƙauna da kuma kyautata musu. (1 Tas. 5:15) Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”—Yoh. 13:35.
16. Ta yaya dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa ta nuna yadda yake ƙaunar mutanensa?
16 Wata doka da Jehobah ya ba Isra’ilawa za ta taimaka mana mu san yadda ya kamata mu bi da ’yan’uwa a ikilisiya. Jehobah ya gaya musu cewa su yi amfani da kayayyakin da ke haikalin don bautarsa kaɗai. Dokar ta nuna yadda za su kula da kayayyakin kuma ta ce duk mutumin da ya karya dokar zai mutu. (L. Ƙid 1:50, 51) Idan Jehobah ya kāre kayayyakin nan da ba su da rai, babu shakka, zai fi kāre bayinsa da ya zaɓa kuma suka yi alkawarin bauta masa! Akwai lokacin da Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa: “Duk wanda ya taɓa mutanena ya taɓa ƙwayar idona ne.”—Zak. 2:8.
17. Ga mene ne Jehobah yake “kasa kunne ya lura”?
17 Malakai ya ce Jehobah yana “kasa kunne ya lura” yayin da mutanensa suke cuɗanya da juna. (Mal. 3:16) Babu shakka, Jehobah ya “san waɗanda suke nasa.” (2 Tim. 2:19) Ya san dukan abin da muke yi da kuma furucinmu. (Ibran. 4:13) Idan mun bi da ’yan’uwanmu yadda bai dace ba, Jehobah yana “kasa kunne ya lura” da hakan. Bugu da ƙari, idan muna nuna musu karimci da gafarta musu da kuma kyautata musu, Jehobah yana lura da haka.—Ibran. 13:16; 1 Bit. 4:8, 9.
JEHOBAH ‘BA ZAI YASHI JAMA’ARSA BA’
18. Ta yaya za mu nuna godiya ga Jehobah don gatan da ya ba mu?
18 Hakika, muna so mu nuna godiya ga Jehobah don gatan da ya ba mu mu zama bayinsa. Mun san cewa alkawarin da muka yi na bauta wa shi kaɗai, shawara ce mafi muhimmanci da muka yanke. Duk da yake muna rayuwa a “muguwar tsara masu rayuwar kwana-kwana,” muna so mutane su ga cewa mu “marasa laifi” ne kuma muna “haskakawa a cikinsu kamar haskoki a duniya.” (Filib. 2:15) Muna ƙin munanan ayyuka. (Yaƙ. 4:7) Muna kuma ƙauna da daraja ’yan’uwanmu Kiristoci domin su ma bayin Jehobah ne.—Rom. 12:10.
19. Ta yaya Jehobah yake yi wa bayinsa albarka?
19 Jehobah ya yi alkawari cewa: “Ba zai yashe jama’arsa ba.” (Zab. 94:14) Babu abin da ya isa ya hana Jehobah cika wannan alkawarin. Ko da wane irin ƙalubalen ne muke fuskanta, har da mutuwa ba ta isa ta hana Jehobah nuna mana ƙauna ba. (Rom. 8:38, 39) Hakika, “idan muna rayuwa, saboda Ubangiji ne muke yi, in kuma mutuwa za mu yi, saboda Ubangiji ne muke yi. Saboda haka ko rayuwa ne muke yi ko mutuwa, mu na Ubangiji ne.” (Rom. 14:8) Babu shakka, muna ɗokin ganin ranar da Jehobah zai tayar da dukan bayinsa daga matattu. (Mat. 22:32) Har ma a yau, muna moran albarku sosai daga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai albarka ce al’ummar da Yahweh shi ne Allahnta, jama’ar da ya zaɓa su zama gādonsa!”—Zab. 33:12.