HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Oktoba 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 27 ga Nuwamba zuwa 24 ga Disamba, 2017.

TARIHI

Za Mu Sami Albarka Idan Muka Yi Abin da Jehobah Yake So

A shekara ta 1952, Olive Matthews da mijinta sun amince su je yin hidima a kasar Ireland. Ta yaya Jehobah ya albarkace su?

“Mu Yi Kauna . . . da Aiki da Gaskiya Kuma”

Ta yaya za mu nuna cewa kaunarmu ta gaskiya ce, ba ta munafunci ba?

Gaskiya Ba ta Kawo ‘Salama, Amma Takobi’

Mene ne “takobi” da yesu ya ce zai kawo. Kuma ta yaya zai shafe ka?

Yusufu Dan Arimathiya ya Kasance da Gaba Gadi

Waye ne wannan mutumin? Mene ne ke tsakaninsa da Yesu? Me ya sa bincika labarinsa yake da kyau?

Darussan da Za Ka Koya Daga Wahayin Zakariya

Littafi mai yawo a sama, an rufe wata mata a cikin kwando, wasu mata biyu suna firewa a sama. Me ya sa Allah ya nuna wa Zakariya irin wannan wahayin?

Karusa da Kambi Suna Kāre Ka

Duwatsu na janganci, karusa da ake yaki da su, kuma an nada babban firist sarki. Wane tabbaci mutanen Allah suka samu daga wahayin Zakariya na karshe?

Sakamako Mai Kyau don Nuna Alheri

Ta yaya aka nuna ma wani da ba ya son Shaidun Jehobah alheri kuma ya soma bauta wa Allah?

Ka Sani?

Me ya sa Yesu ya hana yin rantsuwa?