Ka Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarka!
“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya.”
WAƘOƘI: 52, 65
1-3. Mene ne bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu ta ƙunsa? Ka bayyana.
TUN da yake mu ajizai ne, mukan yi kuskure. Amma Jehobah ba ya yi mana “gwargwadon zunubanmu,” idan muka tuba kuma muka nemi gafara daga gare shi ta wajen hadayar Yesu. (Zab. 103:10) Duk da haka, kamar yadda Dauda ya gaya wa Sulemanu, kafin Jehobah ya karɓi ibadarmu, muna bukatar mu bauta masa da dukan zuciyarmu. (1 Laba. 28:9) Amma a matsayinmu na ajizai ta yaya za mu iya yin hakan?
2 Abin da zai iya taimaka mana mu yi hakan shi ne yin la’akari da yadda rayuwar Sarki Asa ta bambanta da ta Sarki Amaziah. Dukansu sarakunan Yahuda ne kuma sun yi abin da Jehobah yake so, amma Asa ya yi hakan da dukan zuciyarsa. (2 Laba. 15:
4. Mene ne za mu bincika?
4 Don mu fahimci abin da ake nufin da bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu, bari mu duba rayuwar Asa da kuma ta wasu sarakunan Yahuda da suka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya, waɗannan su ne Jehoshafat da Hezekiya da kuma Josiah. Dukan su huɗun sun yi kuskure, amma Jehobah ya amince da su. Me ya sa Jehobah ya ɗauke su a matsayin waɗanda suka bauta masa da dukan zuciyarsu?
ASA YA BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARSA
5. Wane mataki ne Asa ya ɗauka?
5 Bayan an raba masarautar Isra’ila da ta Yahuda, Asa shi ne sarki na uku da ya yi sarauta a Yahuda. Ya kawar da bautar gumaka, bayan haka, sai ya kori mazan da suke karuwanci a haikali daga daularsa gabaki ɗaya. Ƙari ga haka, ya cire kakarsa Maacah a matsayin sarauniya, domin ta yi wata sifar gunki mai-ƙazamta. (1 Ki. 15:
6. Mene ne Asa ya yi sa’ad da Habashawa suka kawo masa hari?
6 Jehobah ya yi wa Yahudawa albarka kuma sun sami kwanciyar hankali. Bayan haka, Zerah Bahabashe ya zo da sojoji guda 1,000,000 da kuma karusa guda 300 don ya yaƙi Yahuda. (2 Laba. 14:
7, 8. Ta yaya za ka yi koyi da Asa a ibadarka ga Jehobah?
7 Dukanmu za mu iya bincika zuciyarmu don mu san ko muna bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Ka tambayi kanka, ‘Shin ina shirye in yi abin da Jehobah yake so, in kāre bauta ta gaskiya kuma in kāre bayin Jehobah daga wani abin da zai iya ɓata dangantakarsu da shi?’ Ka yi tunanin irin gaba gaɗin da Asa ya kasance da shi kafin ya yi abin da ya yi wa Maacah wadda “sarauniya” ce a ƙasar! Babu shakka, wataƙila ba ka taɓa ganin wani da ya yi irin abin da ta yi ba, amma wani yanayi zai iya tasowa da ya kamata ka
nuna irin gaba gaɗin Asa. Alal misali, idan ɗan’uwanka ko kuma abokinka ya yi zunubi kuma ya ƙi tuba, har aka yi masa yankan zumunci, me za ka yi? Shin za ka ɗau matakin daina yin tarayya da shi ne? Mene ne zuciyarka za ta sa ka yi?8 Kamar Asa za ka iya nuna cewa kana bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka idan ka dogara da shi sa’ad da kake fuskantar tsanantawa sosai har da waɗanda kake gani ba za ka iya shawo kansu ba. Zai yiwu a riƙa zolayarka a makaranta don kai Mashaidin Jehobah ne, ko kuma abokan aikinka suna iya yi maka dariya don ka ɗauki hutu don ibada, ko don ba ka yawan karɓan ƙarin aiki bayan an tashi. A irin wannan yanayin ka yi wa Allah addu’a kamar yadda Asa ya yi. Kuma ka dogara ga Jehobah ka ci gaba da yin abin da ya dace. Ƙari ga haka, ka tuna cewa kamar yadda Allah ya ƙarfafa Asa kuma ya taimake shi, kai ma zai yi maka hakan.
9. Sa’ad da muke wa’azi, ta yaya za mu nuna cewa muna bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu?
9 Bayin Allah ba sa tunanin kansu kawai. Asa ya sa mutane sun soma bauta wa Jehobah. Mu ma muna taimaka wa mutane su zo su “biɗi Ubangiji.” Babu shakka, Jehobah yana farin ciki sa’ad da ya ga muna koya wa maƙwabtanmu da sauran mutane game da shi. Kuma muna yin hakan don muna ƙaunarsa kuma muna so mutane su sami rai na har abada!
JEHOSHAPHAT YA BIƊI JEHOBAH
10, 11. Ta yaya za ka iya yin koyi da Jehoshaphat?
10 Jehoshaphat “ya yi tafiya cikin hanyar Asa ubansa.” (2 Laba. 20:
11 A yau, Jehobah yana so mutane a dukan duniya su san shi. Kuma dukanmu za mu iya taimaka wajen yin hakan. Shin burinka ne kowane wata ka riƙa koya wa mutane Kalmar Allah don su bauta masa? Idan kana wa’azi da ƙwazo, za ka iya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Shin kana yin addu’a game da yin hakan? Shin za ka iya yin amfani da lokacinka don yin hakan? Kamar yadda Jehoshaphat ya je biranen Ifraimu don ya taimaka wa mutane su komo ga yin bauta ta gaskiya, mu ma za mu iya taimaka wa waɗanda suka yi sanyin gwiwa. Ƙari ga haka, dattawan ikilisiya suna kai ziyara don su taimaka wa waɗanda aka yi wa yankan zumunci amma daga baya suka tuba.
12, 13. (a) Sa’ad da Jehoshaphat yake fuskantar mawuyacin yanayi, mene ne ya yi? (b) Me ya sa ya kamata mu yi koyi da Jehoshaphat?
12 Ko da yake sojoji masu yawa sun kawo wa Yahuda hari, Jehoshaphat ya dogara ga Jehobah kamar mahaifinsa. (Karanta 2 Labarbaru 20:
13 Kamar Jehoshaphat mukan sami kanmu a wani irin yanayin da ba za mu san abin da za mu yi ba, har ma mu riƙa jin tsoro. (2 Kor. 4:
HEZEKIYA YA CI GABA DA YIN ABIN DA YA DACE
14, 15. Ta yaya Hezekiya ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa?
14 Hezekiya wani sarki ne da ya “manne wa Ubangiji” ko da yake mahaifinsa bai kafa masa misali mai kyau ba, domin ya bauta wa gumaka. Amma Hezekiya “ya kawar da masujadai, ya kakkarya su umudai, ya farfashe maciji na jan ƙarfe, wanda Musa ya ƙera,” domin ‘ya’yan Isra’ila sun soma bauta wa gunki. Hezekiya ya dogara ga Jehobah kuma ya ci gaba da ‘kiyaye umurnansa waɗanda Ubangiji ya umurta wa Musa.’
15 Har ma a lokacin da Assuriyawa waɗanda suke da ƙarfi sosai suka zo su yaƙi Yahuda da kuma Urushalima, Hezekiya ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa. Ƙari ga haka, Sennacherib, Sarkin Assuriya ya faɗi abubuwa marar daɗi game da Jehobah kuma ya nemi Hezekiya ya miƙa wuya. Amma Hezekiya ya dogara ga Jehobah kuma ya nemi taimakonsa. (Karanta Ishaya 37:
16, 17. Ta yaya za ka yi koyi da Hezekiya a bautarka ga Jehobah?
16 Daga baya, Hezekiya ya soma rashin lafiya sosai har ya kusan mutuwa. Sai ya roƙi Jehobah ya tuna da yadda ya yi masa biyayya. (Karanta 2 Sarakuna 20:
17 Ta yaya za mu bi misalin Hezekiya? Za mu yi hakan ta wurin daina yin abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah kuma ya hana mu mai da hankali ga ibadarmu. Saboda haka, bai kamata mu yi koyi da mutanen duniya da suke yin amfani da shafuffukan sada zumunta suna ɗaukaka mutane kamar gumaka ba. Hakika, wasu Kiristoci suna jin daɗin yin amfani da hanyar nan don su riƙa tattaunawa da iyalinsu ko kuma abokansu. Amma mutane da yawa a duniya suna amfani da kafofin sada zumunta don su yi tarayya da maza da mata da ba su sani ba, ko kuma su riƙa ɓata lokaci suna kallon hotuna ko kuma karanta labaran mutane. Za mu iya zama masu fahariya saboda mutane da yawa suna son hotunan da muka saka a irin waɗannan wuraren, A. M. 18:
JOSIAH YA BI DOKOKIN JEHOBAH
18, 19. Ta wace hanya ce za ka yi koyi da Josiah?
18 Jikan Hezekiya, wato Sarki Josiah ya bi dokokin Jehobah da “dukan zuciyarsa.” (2 Laba. 34:31) A lokacin da yake matashi, Josiah “ya soma neman Allah na ubansa Dawuda,” kuma a lokacin da ya kai shekara ashirin ya soma kawar da dukan gumakan da ke Yahuda. (Karanta 2 Labarbaru 34:
19 Matasa suna bukatar su soma bin Jehobah tun suna ƙanana kamar yadda Josiah ya yi. Wataƙila bayan Sarki Manasseh ya tuba, ya koya wa Josiah cewa Jehobah mai jin kai ne. Matasa, kuna bukata ku kusaci tsofaffi da suke iyalinku da kuma ikilisiyarku don ku koyi yadda Jehobah ya kula da su. Ƙari ga haka, ku tuna cewa karatun Littafi Mai Tsarki ne ya taɓa zuciyar Josiah kuma ya sa shi ya yi ƙwazo a bautarsa ga Jehobah. Karanta Littafi Mai Tsarki zai sa ku kasance da ƙwazo a bautarku ga Jehobah. Ban da haka, karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku ku yi farin ciki kuma ku ci gaba da ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Hakan zai taimaka ma wasu ma su san shi. (Karanta 2 Labarbaru 34:
KA BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA!
20, 21. (a) Mene ne sarakuna huɗun suka yi? (b) Mene ne za mu bincika a talifi na gaba?
20 Shin nazarin yadda sarakuna huɗun nan suka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu ya amfane ka? Sun sa ƙwazo sosai a hidimarsu ga Jehobah kuma sun ci gaba da bauta masa. Ƙari ga haka, sun yi hakan har a lokacin da maƙiyansu suke so su kawo musu hari. Amma mafi muhimmanci, sun bauta wa Jehobah domin suna ƙaunarsa.
21 Ko da yake sarakuna huɗun nan sun yi kuskure, Jehobah ya amince da su. Ya ga abin da yake zuciyarsu kuma ya san cewa suna ƙaunarsa da gaske. Mu ma ajizai ne kuma muna kuskure, amma Jehobah zai yi farin ciki idan ya ga cewa muna bauta masa da dukan zuciyarmu. A talifi na gaba za mu bincika abin da muka koya daga kurakuren waɗannan sarakunan.