“Na Sani Za Ya Tashi”
“Abokinmu Li’azaru yana barci; amma zan tafi, domin in tashe shi.”—YOH. 11:11.
1. Wane tabbaci ne Martha take da shi game da ɗan’uwanta? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
ABOKIYAR Yesu mai suna Martha tana makoki. Me ya faru? Ɗan’uwanta Li’azaru ya mutu. Akwai abin da zai iya ƙarfafa ta kuwa? E. Yesu ya ƙarfafa ta, ya ce: “Ɗan’uwanki zai tashi.” Ko da yake hakan bai sa ta daina baƙin ciki da take yi ba, amma ta ce: ‘Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.’ (Yoh. 11:20-24) Furucin da ta yi ya nuna cewa ta tabbata cewa za a yi tashin matattu a nan gaba. Amma Yesu ya yi wata mu’ujiza a ranar. Me ya yi? Ya ta da Li’azaru daga mutuwa.
2. Me ya sa kake son ka kasance da bangaskiya irin ta Martha?
2 Ba za mu zaci Yesu ko Jehobah su riƙa mana mu’ujiza a yau ba. Duk da haka, kana da tabbaci irin na Martha cewa za a yi tashin matattu? Wataƙila mijinki ko matarka ko iyayenka ko kuma kakanka ya rasu. Ko kuma kana baƙin ciki don yaronka ko ’yarka ta rasu. Babu shakka, za ka so ka rungume su don ku yi hira ko kuma ku yi abubuwan da za su sa ku farin ciki tare. Don haka, kai ma kamar Martha za ka iya cewa: ‘Na sani
ɗan’uwana zai tashi a rana ta ƙarshe.’ Amma zai yi kyau kowannenmu ya yi tunani a kan dalilin da ya sa muke da wannan tabbacin.3, 4. Ta yaya wataƙila mu’ujizai da Yesu ya yi ba da daɗewa ba suka ƙarfafa Martha?
3 Da yake Martha tana zama kusa da Urushalima, wataƙila ba ta ga lokacin da Yesu ya ta da ’yar wata gwauruwa a garin Nayin a Galili ba. Mai yiwuwa ta ji mutane suna ba da labarin. Kuma ta wataƙila ta ji labarin yadda Yesu ya ta da ’yar Yayirus. Waɗanda suke gidan da yarinyar take sun san cewa ta “rasu” da gaske. Amma da Yesu ya zo, sai ya riƙe hannunta kuma ya ce: “Yarinya, ki tashi.” Sai nan da nan yarinyar ta tashi. (Luk. 7:11-17; 8:41, 42, 49-55) Martha da ’yar’uwarta Maryamu sun san cewa Yesu yana iya warkar da marasa lafiya. Don haka, sun ɗauka cewa da a ce Yesu yana nan, da Li’azaru bai mutu ba. Da yake abokin Yesu ya riga ya mutu, wane bege suke da shi? Ka yi la’akari da abin da Martha ta faɗa, ta ce ta sani zai tashi a nan gaba, wato a ‘rana ta ƙarshe.’ Me ya sa ta kasance da wannan tabbacin? Kuma me ya sa kai ma za ka kasance da tabbaci cewa za a ta da ’yan’uwanka da suka rasu a nan gaba?
4 Kana da dalilai masu kyau na kasancewa da wannan tabbacin. Yanzu za mu bincika wasu cikin waɗannan dalilan, kuma yayin da muke yin hakan, za ka ga wasu abubuwa a Littafi Mai Tsarki da suke da alaƙa da begen tashin matattu da ba ka taɓa yin tunani a kansu ba.
ABUBUWAN DA SUKE SA MU KASANCE DA BEGE!
5. Me kuma ya tabbatar wa Martha cewa za a ta da ɗan’uwanta Li’azaru?
5 Ka lura cewa Martha ba ta ce: ‘Ina da begen cewa ɗan’uwana zai tashi’ ba, amma ta ce, ‘na sani za ya tashi.’ Martha ta tabbata da hakan don ta san labaran wasu mu’ujizai da bayin Allah suka yi tun kafin Yesu ya soma hidimarsa a duniya. Iyayenta sun koya mata hakan kuma idan ta je majami’a ma takan koyi hakan. Wataƙila tana sane da labaran mutane uku da aka ba da a Nassosi.
6. Wace mu’ujiza ce Iliya ya yi, kuma ta yaya hakan ya shafi Martha?
6 Labari na farko na wani da aka ta da daga mutuwa ya faru ne a lokacin da Allah ya ba wa annabi Iliya ikon yin mu’ujizai. A Zarefat da ke garin Finikiya, akwai wata gwauruwa matalauciya da ta karɓi annabi Iliya a gidanta. Sai Jehobah ya sa kada gārinta da manta su ƙare don ita da ɗanta kada su mutu. (1 Sar. 17:8-16) Ana nan wata rana, sai ɗanta ya yi ciwo kuma ya mutu. Me Iliya ya yi? Iliya ya taɓa gawar kuma ya yi addu’a, ya ce: “Allahna, ina roƙonka, ka bar ran yaron nan ya sāke shiga cikinsa.” Allah ya ji addu’ar Iliya kuma yaron ya rayu. Wannan shi ne lokaci na farko da aka ta da wani daga mutuwa a Littafi Mai Tsarki. (Karanta 1 Sarakuna 17:17-24.) Babu shakka, Martha ta san da wannan labarin.
7, 8. (a) Ka faɗi abin da Elisha ya yi don ya taimaka ma wata mata da take makoki. (b) Me mu’ujizar da Elisha ya yi ta tabbatar mana game da Jehobah?
7 Labarin tashin matattu na biyu da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne wanda annabi Elisha wanda ya gāji Iliya ya yi. Wata Ba-isra’iliya da aka san ta sosai a garin Shunem ta karɓi Elisha da kyau sa’ad da ya zo gidansu. Kuma Jehobah ya yi amfani da wannan annabin don ya sa wannan mata da mijinta su haifi yaro da yake ba su da yaro a lokacin. Bayan wasu shekaru, sai yaron ya mutu. 2 Sar. 4:8-31.
Mahaifiyar yaron ta yi baƙin ciki sosai. Ta nemi izini daga maigidanta kuma ta yi tafiyar kilomita 30 zuwa Dutsen Karmel wurin Elisha. Annabin ya tura bawansa mai suna Gehazi zuwa Shunem don ya ta da yaron kafin su iso, amma ya kāsa ta da shi. Sai annabin da mahaifiyar yaron suka iso wurin.—8 Bayan haka, sai Elisha ya yi addu’a a kan gawar yaron. Sai me ya faru? Mataccen yaron ya tashi kuma aka miƙa shi ga mahaifiyarsa kuma ta yi murna sosai! (Karanta 2 Sarakuna 4:32-37.) Ban da haka ma, wataƙila Martha ta tuna da addu’ar da Hannatu ta taɓa yi sa’ad da ta kawo Sama’ila ya yi hidima a mazauni, ta ce: “Ubangiji . . . yakan ƙasar da wani har kabari, yakan kuwa tayar.” (1 Sam. 2:6) Babu shakka, yadda Allah ya ta da yaron matar Shunem ya nuna cewa yana da ikon ta da mutane da suka mutu.
9. Ka faɗi yadda tashin matattun na uku a Littafi Mai Tsarki ya shafi Elisha.
9 Amma wannan ba shi ne mu’ujiza na ƙarshe da Elisha ya yi ba. Ya yi hidimar annabi fiye da shekaru 50 kuma bayan haka, sai Elisha ya yi ciwo mai tsanani kuma ya “mutu.” Amma bayan da aka binne Elisha kuma ya zama ƙasusuwa, sai magabta suka shigo cikin ƙasar. Wasu Isra’ilawa sun je don su binne wani mutum, sai suka hangi magabtansu suna zuwa. Da suka ga hakan, sai suka yar da gawar a kabarin da aka binne Elisha kuma suka gudu. Me ya faru? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da mutumin ya taɓa ƙasusuwan Elisha, sai ya wartsake, ya tsaya bisa ƙafafunsa.” (2 Sar. 13:14, 20, 21) Babu shakka, waɗannan labaran sun taimaka wa Martha sosai, ko ba haka ba? Allah yana da iko ya ta da mutanen da suka mutu. Kuma yin tunani a kan irin waɗannan labaran za su taimaka mana a yau. Ban da haka ma, za su taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa ikon Allah ba shi da iyaka.
ABUBUWAN DA SUKA FARU A ƘARNI NA FARKO
10. Mene ne ya faru da Tabita, kuma mene ne Bulus ya yi?
10 Muna da labaran mutanen da aka ta da daga mutuwa a Nassosin Helenanci na Kirista da wasu bayin Allah suka shaida. Waɗannan labaran su ne na mutanen da Yesu ya ta da a bayan garin Nayin da kuma wanda ya ta da a lokacin da ya je gidan Yayirus. Manzo Bitrus ma ya ta da wata mata mai suna Dokas, wato Tabita. Bitrus ya zo wurin da aka ajiye gawar sai ya yi addu’a. Bayan haka, sai ya ce: “Tabita, ki tashi.” Nan da nan sai ta tashi kuma Bitrus ya kirawo wasu Kiristoci “ya miƙa masu ita da rai.” Hakan ya sa “mutane da yawa kuwa suka ba da gaskiya ga Ubangiji.” Don sun ga cewa Yesu da kuma musamman Jehobah suna da ikon ta da matattu.—A. M. 9:36-42.
11. Me likitan nan Luka ya ce ya faru da wani matashi, kuma yaya waɗanda suka ga yadda aka ta da shi suka ji?
11 Akwai wasu ma da suka shaida yadda aka ta da wani daga mutuwa. Wata rana Bulus yana tattaunawa da wasu a wani bene a garin Taruwasa da yanzu yake arewa maso gabashin Turkiya. Bulus ya yi jawabi har cikin dare. Wani matashi mai suna Aftikos yana cikin masu sauraron kuma yana zaune a kan taga. Da barci ya ɗauke shi, sai ya faɗi a ƙasa. Wataƙila likitan nan Luka ne ya fara sauƙowa ƙasa kuma ya yi bincike irin nasu na likitoci sai ya ga cewa Aftikos ba rauni ya ji ba, amma ya mutu! Da Bulus ya sauƙo, sai ya rungumi gawar kuma ya ce: “Ransa yana cikinsa.” Waɗanda suka shaida hakan sun yi mamaki sosai. Abin A. M. 20:7-12.
al’ajabin da suka gani ya sa sun “sami ta’aziyya ba kaɗan ba.”—TABBATACCEN BEGE
12, 13. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika bisa ga abin da muka tattauna game da tashin matattu?
12 Labaran waɗanda da aka ta da daga mutuwa za su sa ka kasance da tabbaci irin na Martha cewa Allah wanda shi ne ya ba da rai yana da ikon ta da mutumin da ya mutu. Amma a lokacin da Jehobah ya ta da mutane daga mutuwa, bayinsa kamar su Iliya da Yesu da Bitrus duk sun shaida hakan. To, me zai faru da mutanen da suka mutu da a zamaninsu ba a taɓa yin mu’ujizar tashin matattu ba? Tun da yake akwai lokacin da Allah ba ya ta da mutane daga mutuwa, shin mutane masu aminci za su iya zama da tabbaci cewa a nan gaba zai yi hakan ne? Za su ji kamar yadda Martha ta ji sa’ad da ta ce: ‘Na sani ɗan’uwana zai tashi a rana ta ƙarshe’? Me ya sa ta gaskata cewa hakan zai faru, kuma me ya sa kai ma za ka yi hakan?
13 Akwai wurare da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa bayin Allah a dā sun tabbata cewa za a yi tashin matattu a nan gaba. Bari mu bincika kaɗan daga cikinsu.
14. Wane darasi za mu koya game da tashin matattu daga labarin Ibrahim?
14 Ka yi la’akari da abin da Allah ya gaya wa Ibrahim ya yi da ɗansa Ishaƙu tilo wanda zai gāje shi. Jehobah ya ce: “Sai ka ɗauki ɗanka, tilonka, wanda kake ƙaunarsa, wato Ishaƙu” . . . ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa.” (Far. 22:2) Wannan furucin da Jehobah ya yi zai sa Ibrahim cikin tunani sosai. Me ya sa? Domin Jehobah ya yi alkawari cewa ta wurin zuriyar Ibrahim ne dukan al’ummar duniya za su yi albarka. (Far. 13:14-16; 18:18; Rom. 4:17, 18) Ban da haka ma, Jehobah ya ce ta wurin “Ishaƙu” ne za a sami albarka. (Far. 21:12) Amma ta yaya hakan zai yiwu idan Ibrahim ya yi hadaya da ɗansa Ishaƙu? Da taimakon ruhun Allah, Bulus ya ce Ibrahim ya gaskata cewa Allah zai iya ta da Ishaƙu daga mutuwa. (Karanta Ibraniyawa 11:17-19.) Amma Littafi Mai Tsarki bai ce Ibrahim yana ganin cewa idan ya yi biyayya, bayan wasu sa’o’i ko kwana ɗaya ko mako ɗaya Ishaƙu zai rayu ba. Ibrahim bai san lokacin da Allah zai ta da ɗansa daga mutuwa ba. Duk da haka, ya gaskata cewa Jehobah zai ta da Ishaƙu.
15. Wane bege ne Ayuba yake da shi?
15 Ayuba ya gaskata cewa za a yi tashin Ayu. 14:7-12; 19:25-27) Idan mutum ya mutu, ba zai iya ta da kansa ba. (2 Sam. 12:23; Zab. 89:48) Amma hakan ba ya nufin cewa Allah ba zai iya ta da mutumin da ya rasu ba. Babu shakka, Ayuba ya gaskata cewa Jehobah ya ƙayyade lokacin da zai tuna da shi. (Karanta Ayuba 14:13-15.) Amma bai san ainihin lokacin ba. Duk da haka, ya gaskata cewa wanda ya halicci mutane ba zai manta ya ta da shi daga mutuwa ba.
matattu a nan gaba. Ya san cewa idan aka yanke itace, zai sake tohuwa ya zama itace. Amma, ba haka yake da mutane ba. (16. Wane tabbaci ne wani mala’ika ya ba wa Daniyel?
16 Daniyel wani ne da aka ba da labarinsa a cikin Nassosin Ibrananci. Ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah da aminci kuma Jehobah ya taimaka masa. Amma akwai lokacin da wani mala’ika ya gaya wa Daniyel “ƙaunatacce” ya kasance da “salama” kuma ya yi “ƙarfi.”—Dan. 9:22, 23; 10:11, 18, 19.
17, 18. Wane alkawari aka yi wa Daniyel game da nan gaba?
17 Daniyel ya kusan shekara 100 kuma ya kusan mutuwa. Wataƙila yana tunanin abin da zai faru da shi a nan gaba. Shin za a ta da shi daga mutuwa kuwa? Ƙwarai kuwa! A ƙarshen littafin Daniyel, Allah ya ba shi tabbacin hakan kuma ya ce: “Ka yi tafiyarka ka huta.” (Dan. 12:13, Littafi Mai Tsarki) Daniyel ya san cewa matattu ba su da ‘dabara ko ilimi ko hikima a cikin kabari.’ Kuma wurin ne Daniyel zai je ba da daɗewa ba. (M. Wa. 9:10) Amma ba za a bar shi a wurin ba domin an yi masa alkawari cewa za a ta da shi a nan gaba.
18 An ƙara gaya wa Daniyel cewa: “A ƙarshen kwanaki, za ka tashi ka karɓi naka rabo.” Ba a gaya masa daidai lokacin da za a masa hakan ba. An gaya wa Daniyel cewa zai mutu kuma ya huta. Duk da haka, abin da aka gaya masa cewa zai sami “rabo” a nan gaba ya nuna cewa yana da begen tashi daga mutuwa. Kuma za a ta da shi “a ƙarshen kwanaki.”
19, 20. (a) Ta yaya abin da muka bincika yake da alaƙa da abin da Martha ta gaya wa Yesu? (b) Me za mu bincika a talifi na gaba?
19 Babu shakka, Martha tana da tabbaci cewa ɗan’uwanta mai aminci “zai tashi a rana ta ƙarshe.” Alkawarin da aka yi wa Daniyel da kuma amsar da Martha ta ba wa Yesu za su sa mu kasance da tabbaci cewa za a ta da matattu.
20 Daga abubuwan da muka tattauna, mun ga cewa labaran mutanen da aka ta da daga mutuwa ya tabbatar mana da cewa babu abin da zai hana Allah ta da matattu. Bayin Allah maza da mata sun kasance da bege cewa za a yi tashin matattu a nan gaba. Akwai wani abu da ya tabbatar mana cewa za a ta da matattu ko da yake an yi annabcin hakan tun da daɗewa? Idan haka ne, muna da dalilai masu kyau na kasancewa da bege kamar Martha cewa za a yi tashin matattu. Amma yaushe hakan zai faru? Za mu bincika hakan a talifi na gaba.