Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za Ka Iya Cin Nasara!

Za Ka Iya Cin Nasara!

Za Ka Iya Cin Nasara!

LOKACI ya yi da za ka “yi karfin zuciya” kuma ka dau mataki. (1 Tarihi 28:10) Wadanne matakai ne za su kara taimaka maka ka yi nasara?

Ka sa ranar da za ka daina. Ma’aikatar lafiya ta Amirka mai suna U.S. Department of Health and Human Services, ta ce da zarar ka yanke shawarar daina shan taba, ya kamata a ce cikin sati biyu, ka sami rana guda da ka wuni kuma ka kwana ba ka sha sigari ba. Hakan zai taimaka maka ka tsaya a kan bakarka na dainawa. Ka māka ranar da za ka daina shan sigari a kalanda kuma ka gaya wa abokanka. Kar ka canja ranar ko da me ya faru.

Ka rubuta wasu bayanai da za su taimaka maka ka daina. Ka nemi takarda kuma ka rubuta duk wani abin da ka san zai kara maka kwarin gwiwar dainawa. Za ka iya rubuta abubuwa kamar:

● Dalilan da suka sa kake so ka daina sha

● Lambobin wadanda da za ka kira idan jarabar tana so ta fi karfinka

● Kalaman da idan ka karanta, za su kara maka kwarin gwiwa. Alal misali za ka iya rubuta nassosi irinsu Galatiyawa 5:​22, 23

Ka dinga yawo da takarda ko katin da ka rubuta abubuwan nan a kai, kuma ka dinga karanta su sau da yawa kowace rana. Ko da ka yi nasara wajen daina sha, ka sake karanta katin a duk lokacin da ka ji kwadayin shan taba.

Ka soma canja duk wani tsari da kake bi dangane da shan taba. Yayin da ranar da za ka daina yake gabatowa, ka soma canja abubuwan da kake yi dangane da shan taba. Alal misali, idan ka saba shan taba da zarar ka tashi da safe, ka dan jira sai bayan wajen awa guda. Idan kuma ka saba shan taba yayin da kake cin abinci ko da zarar ka gama ci, ka koma sha a wani lokaci dabam. Ka kauce ma wurare da ake shan taba. Kuma ka yi ta koyan yadda za ka furta cewa: “A’a kar ka damu, na daina shan taba!” Matakan nan za su taimaka maka ka yi shiri don ranar da za ka daina shan taba. Za su kuma tuna maka cewa nan ba da dadewa ba, za ka rabu da shan sigari.

Ka yi shiri. Idan ranar da za ka daina shan sigari ya kusa, ka sayi abubuwa kamar su karas, da cingam, da gyada da dai sauransu, ka ajiye. Ka sake tuna wa abokanka da danginka ranar da kake so ka daina shan sigari, da abin da za su yi don su taimaka maka. Ana washegari za ka daina shan sigari, ka tattara farantin da kake sa tokar sigari, da su ashana, da leta (lighter), da duk wani raguwar sigari da ke dakinka ko aljihunka ko motarka ko wurin aikinka, ka zubar. Hakan zai kara sa ya yi maka sauki ka daina. Kari ga haka, ka ci-gaba da addu’a kana rokon Allah ya taimake ka. Musamman bayan ka sha sigarinka na karshe.​—Luka 11:13.

Akwai mutane da yawa da suka rabu da shan sigari. Kai ma za ka iya. Idan ka yi hakan, za ka sami ’yanci kuma za ka kyautata lafiyar jikinka.

[Hoto]

Ka dinga yawo da kati ko takardar da ka rubuta bayanan da za su taimaka maka ka daina sha, kuma ka dinga karanta su a kai a kai yayin da kake harkokinka na yau da kullum