Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
An shirya wannan littafin don ya taimaka muku ku kyautata yadda kuke karatu da magana da kuma koyarwa.
Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
Muna ba wa mutane sako mafi muhimmanci da Allah ya taba ba wa ’yan Adam.
DARASI NA 2
Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa
Ka yi kamar kuna tattaunawa don hakan zai sa masu sauraronka su sake jiki da kai kuma su amince da abin da kake faɗa kuma.
DARASI NA 3
Ka Yi Amfani da Tambayoyi
Ka yi tambaya da basira don ka ja hankalin masu sauraronka ko ka taimaka musu su fahimci batun da kake tattaunawa.
DARASI NA 4
Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace
Kafin ka karanta wani nassi, ka yi kokari ka sa masu sauraronka marmarin nassin kafin ka karanta shi.
DARASI NA 5
Ka Yi Karatu Sumul
Yin karatu sumul yana da muhimmanci sosai wajen koyar da Kalmar Allah.
DARASI NA 6
Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
Ka sa masu sauraronka su ga yadda nassin ya jitu da abin da kake gaya musu.
DARASI NA 7
Ka Koyar da Gaskiya
Idan ka ba da tabbaci cewa abin da kake koyarwa gaskiya ne, hakan zai sa masu sauraronka su gaskata da abin da kake fada.
DARASI NA 8
Misalai Masu Amfani
Ka inganta koyarwarka da misalai masu sauki da za su ratsa zuciyar masu sauraro. Misalan su koyar da darussa masu muhimmanci.
DARASI NA 9
Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ake Gani
Ka yi amfani da abubuwan da ido ke gani don a fahimci muhimman darussa da kake son masu sauraronka su tuna da su.
DARASI NA 10
Muryar da Ta Dace
Hakan yana nufin cewa ka rika canja murya ko ka daga murya ko kuma ka rage sauri ko kara sauri don ka motsa masu souraronka su aikata abin da suka koya.
Darasi na 11
Ka Yi Magana da Kuzari
Yin magana da kuzari zai nuna yadda kake ji game da batun kuma zai jawo hankalin masu sauraronka.
DARASI NA 12
Ka Nuna Kauna da Tausayi
Idan kana magana da tausayi, hakan zai nuna wa masu sauraronka cewa ka damu da su da gaske.
DARASI NA 13
Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci yadda batun da kake tattaunawa ya shafe su kuma ka nuna abin da ya kamata su yi.
DARASI NA 14
Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla
Ka taimaka wa masu sauraronka su rika bin jawabin, kuma ka nuna musu yadda muhimman bayanan suka jitu da jigon da kuma darasin.
DARASI NA 15
Ka Yi Magana Ba Shakka
Ka yi magana ba shakka. Ka nuna cewa maganarka gaskiya ce kuma tana da muhimmanci sosai.
DARASI NA 16
Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa
Ka fadi abubuwan karfafa ba munana ba. Ka sa masu sauraronka su fahimci abubuwan da za su karfafa su da ke Kalmar Allah.
DARASI NA 17
Ka Yi Bayani Dalla-Dalla
Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci sakon da kake son ka ba su. Ka bayyana muhimman darussa dalla-dalla.
DARASI NA 18
Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
Ka sa su yi tunani a kan batun da kake gaya musu kuma su ji sun koyi darussa masu muhimmanci.
DARASI NA 19
Maganarka ta Ratsa Zuciya
Ka taimaka wa masu sauraro su kaunaci Jehobah kuma su so koyarwar Littafi Mai Tsarki.
DARASI NA 20
Kammalawa Mai Dadi
Kammalawa mai dadi zai taimaka wa masu sauraro su amince da abin da ka fada kuma su yi amfani da shi.
Ka Rubuta Ci Gaban da Ka Samu
Ka rubuta ci gaban da ka samu yayin da kake kokarin kyautata yadda kake karatu da kuma koyarwa.
Mai Yiwuwa Za Ka Kuma So
VIDEO SERIES
Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa—Bidiyoyi
Ka koyi yadda za ka yi karatu da kuma koyarwa a gaban jama’a.