Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 7

Ikon Kāriya—Allah “Wurin Buyanmu” Ne

Ikon Kāriya—Allah “Wurin Buyanmu” Ne

1, 2. Isra’ilawa suna cikin wane haɗari sa’ad da suka shiga cikin yankin Sinai a shekara ta 1513 K.Z., kuma yaya Jehobah ya ba su tabbaci?

 ISRA’ILAWA suna cikin haɗari sa’ad da suka shiga yankin Sinai a farkon shekara ta 1513 K.Z. Tafiya mai ban tsoro yana gabansu, tafiya cikin “babban jeji, mai-ban tsoron nan, wurinda macizai masu-wuta su ke, da kunamai.” (Maimaitawar Shari’a 8:15) Sun fuskanci burga daga al’ummai masu hamayya. Jehobah ya sa mutanensa cikin wannan yanayin. Tun da Allahnsu ne, zai iya kāre su kuwa?

2 Kalmomin Jehobah suna ba da tabbaci: “Kun ga abin da na yi wa Masarawa, da kuma yadda na ɗauke ku na kawo ku wurina kamar yadda gaggafa take ɗaukar ’ya’yanta.” (Fitowa 19:4) Jehobah ya tunasar da mutanensa cewa ya cece su daga Masarawa, ya yi amfani da gaggafa, cikin alama ya ɗauko su su tsira. Amma kuma da akwai wasu dalilai da ya sa “gaggafa” suka dace wajen kwatanta kāriya daga Allah.

3. Me ya sa “gaggafa” sun dace wajen kwatanta kāriyar Allah?

3 Gaggafa tana amfani da fukafukanta masu girma, masu ƙarfi fiye da ta tashi sama kawai. Sa’ad da rana take da zafi, gaggafa za ta miƙe fukafukanta—da zai kai wajen ƙafa bakwai—ta yi laima, ta kāre ’yan ƙanananta daga zafin rana. A wani lokaci, tana kewaye ’yan ƙanananta da fukafukanta ta kāre su daga iska mai sanyi. Kamar yadda gaggafar take kāre ’yan ƙanananta, haka Jehobah ya kāre ƙaramar al’ummar Isra’ila. Yanzu a daji, mutanensa za su ci gaba da fakewa a inuwar fukafukinsa mai girma muddin sun ci gaba da aminci. (Maimaitawar Shari’a 32:9-11; Zabura 36:7) Amma daidai ne mu yi tsammanin kāriyar Allah a yau?

Alkawarin Kāriyar Allah

4, 5. Me ya sa za mu dogara ga alkawarin Allah na kāriya?

4 Babu shakka, Jehobah zai iya kāre bayinsa. Shi ne “Allah Mai Iko Duka”—laƙabi da ya nuna cewa yana da iko da babu iyaka. (Farawa 17:1) Kamar malalar teku, ikon da Jehobah ya sa a aiki ba za a iya wargaje shi ba. Tun da zai iya yin duk abin da ya nufa, za mu iya tambaya, ‘Nufin Jehobah ne ya yi amfani da ikonsa ya kāre mutanensa?’

5 E! Jehobah ya tabbatar mana cewa zai kāre mutanensa. Zabura 46:1 ta ce: “Allah shi ne wurin ɓuyanmu da ƙarfinmu, taimakonmu na kurkusa lokacin wahala.” Tun da Allah “ba ya ƙarya,” za mu iya dogara ga alkawarinsa na kāriya. (Titus 1:2) Bari mu bincika wasu kwatanci da Jehobah ya yi amfani da su wajen kwatanta kāriyarsa.

6, 7. (a) Makiyayi na lokatan Littafi Mai Tsarki yana ba da wace kāriya ce ga tumakinsa? (b) Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta muradin Jehobah na kāre mu da kuma kula da tumakinsa?

6 Jehobah makiyayi ne, kuma “mu mutanensa ne, kuma garken kiwonsa.” (Zabura 23:1;100:3) Dabbobi kaɗan ne kawai ba su da kāriya kamar tumaki. Makiyayi na lokatan Littafi Mai Tsarki dole ne ya mazakuta ya kāre tumakinsa daga zakuna, karnukan daji, da kuma ɓarayi. (1 Sama’ila 17:34, 35; Yohanna 10:12, 13) Amma akwai lokacin da kāre tumakin yana bukatar hankali. Idan tunkiya ta haihu nesa da garke, makiyayi mai ƙauna zai yi gadin uwar, a wannan lokacin kuma ya ɗauki ɗan tunkiyar marar ƙarfi zuwa garken.

“Ya rungume su a ƙirjinsa”

7 Ta wajen kwatanta kansa da makiyayi, Jehobah ya tabbatar mana muradinsa na son ya kāre mu. (Ezekiyel 34:11-16) Ka tuna kwatancin Jehobah da aka samu a Ishaya 40:11, da aka tattauna a Babi na 2 na wannan littafin: “Yana ciyar da tumakinsa kamar yadda makiyayi yake yi. Yana tara ’yan tumakin a hannuwansa, ya rungume su a ƙirjinsa.” Ta yaya ɗan tunkiya ya kasance a “ƙirjin” makiyayin—a ninki na saman rigarsa? Ɗan tunkiyar zai je ga makiyayin, har ma ya shafi ƙafarsa. Amma, makiyayin ne dole ya sunkuya, ya ɗauki ɗan tunkiyar, kuma ya ɗaura shi a ƙirjinsa wajen kāriya a hankali. Wannan kwatanci ne mai kyau na son ran Makiyayinmu Mai Girma ya yi mana mafaka kuma ya kāre mu!

8. (a) Alkawarin kāriyar Allah an miƙa wa wanene, kuma yaya aka nuna wannan a Misalai 18:10? (b) Mene ne samun mafaka cikin sunan Allah ya ƙunsa?

8 Alkawarin kāriyar Allah, yana bisa sharaɗi ne—waɗanda suka matso kusa da shi ne kawai suke samu. Karin Magana 18:10 ta ce: “Sunan Yahweh katanga mai ƙarfi ne, mai adalci yakan gudu ya shiga ya zauna lafiya.” A lokatan Littafi Mai Tsarki, wani lokaci ana gina hasumiya a daji, watau, wajen mafaka ce. Amma hakkin wanda yake cikin haɗari ne ya ruga zuwa wannan hasumiyar domin ya samu kāriya. Kama yake da neman mafaka cikin sunan Allah. Wannan ya ƙunshi fiye da kiran sunan Allah kawai; sunan Allah ba layar zana ba ce. Maimakon haka, muna bukatar mu sani kuma mu dogara ga Mai sunan kuma mu rayu cikin jituwa da mizanansa na adalci. Jehobah yana da kirki da ya tabbatar mana cewa idan muka juya gare shi cikin bangaskiya, zai kasance hasumiyar kāriya dominmu!

“Allahnmu . . . Yana da Iko Ya Cece Mu”

9. Ta yaya Jehobah ya yi fiye da yin alkawarin kāriya kawai?

9 Jehobah ya yi fiye da yin alkawarin kāriya. A zamanin Littafi Mai Tsarki, ya nuna ta hanyoyin mu’ujiza cewa zai iya kāre mutanensa. Lokacin tarihin Isra’ila, ‘hannu’ mai girma na Jehobah sau da yawa yake korar abokan gaba. (Fitowa 7:4) Amma, Jehobah ya yi amfani da ikonsa na kāriya domin wasu mutane.

10, 11. Wane misali ne ya nuna yadda Jehobah yake amfani da ikonsa na kāriya domin mutane ɗai-ɗai?

10 Sa’ad da samari Ibraniyawa uku—Shadrach, Meshach, da Abednego—suka ƙi su yi sujjada ga gunkin zinariya na Sarki Nebuchadnezzar, sarki da ya fusata ya yi burgar jefa su cikin tanderu mai ƙuna. “Wane allah ne zai kuɓutar da ku daga hannuna,” zolayar Nebuchadnezzar sarki mafi iko a duniya ke nan. (Daniyel 3:15) Matasan uku suna da cikakken tabbaci ga ikon Allahnsu ya kāre su, amma ba su yi tsammanin cewa zai yi haka ba. Saboda haka, suka amsa: “Allahnmu wanda muke bauta wa yana da ikon kuɓutar da mu.” (Daniyel 3:17) Hakika, tanderu mai ƙuna, har ma lokacin da aka ƙara masa wuta sau bakwai fiye da yadda yake, bai zama ƙalubale ba ga Allahnsu mafi iko. Ya kāre su, kuma sarkin an tilasta masa ya fahimci cewa: “Babu wani allah wanda zai iya yin irin wannan kuɓutarwa kamar haka.”—Daniyel 3:29.

11 Jehobah ya ba da kwatanci na musamman na ikonsa na kāriya sa’ad da ya juya ran Ɗansa makaɗaici zuwa cikin budurwa Bayahudiya, Maryamu. Mala’ika ya gaya wa Maryamu cewa za ta yi “ciki” ta “kuma haifi ɗa.” Mala’ikan ya yi bayani: “Ruhu Mai Tsarki zai sauko a kanki, ikon Mafi Ɗaukaka kuma zai rufe ki.” (Luka 1:31, 35) Hakika, Ɗan Allah bai taɓa kasancewa a irin wannan yanayi mai haɗari ba. Shin zunubi da ajizancin uwa talika za su shafi tayin ne? Shaiɗan zai iya ji ma ko kuma ya kashe Ɗan ne kafin a haife Shi? Ba zai yiwu ba! Jehobah ya yi ganuwa, garu domin kāriya ya kewaye Maryamu domin kada kome ya shafe shi—babu ajizanci, babu mugunta, ko kuma mutane masu kisa, ko aljani—da zai iya halaka tayi da yake girma, daga lokacin ɗaukan ciki zuwa gaba. Jehobah ya ci gaba da kāre Yesu lokacin da yake saurayi. (Matiyu 2:1-15) Har sai lokaci da Allah ya ƙa’ide, Ɗansa da yake ƙauna ba abin da za a iya taɓawa ba ne.

12. Me ya sa Jehobah ya kāre wasu mutane a zamanin Littafi Mai Tsarki?

12 Me ya sa Jehobah ya kāre wasu a irin wannan hanya ta mu’ujiza? Ko yaya dai Jehobah ya kāre wasu mutane domin ya kāre abin da ya fi muhimmanci: cika nufinsa. Alal misali, tsirar jariri Yesu tilas ne wajen cika nufin Allah, wanda nan take zai amfani dukan ’yan Adam. Tarihi da yawa da suka nuna iko na kāriya, sashe ne na hurarrun Nassosi, da aka rubuta “domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya ta wurin jimrewa da ƙarfafawa waɗanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.” (Romawa 15:4) Hakika, waɗannan misalai suna ƙarfafa bangaskiyarmu ga Allahnmu mafi iko. Amma wace kāriya za mu yi tsammani daga wajen Allah a yau?

Abin da Kāriyar Allah ba ta Nufa Ba

13. Tilas ne Jehobah ya yi mu’ujiza dominmu? Ka yi bayani.

13 Alkawarin kāriyar Allah ba ya nufin cewa tilas ne Jehobah ya yi mu’ujiza dominmu. A’a, Allahnmu bai ba mu tabbaci na rayuwa marar wahala ba a wannan tsohon zamanin. Bayin Jehobah masu aminci da yawa sun fuskanci wahala mai tsanani, haɗe da talauci, yaƙi, ciwo, da kuma mutuwa. Yesu ya fito fili ya gaya wa almajiransa cewa wasu za a kashe su domin bangaskiyarsu. Wannan shi ne dalilin da ya sa Yesu ya nanata bukatar jimiri har matuƙa. (Matiyu 24:9, 13) Idan Jehobah zai yi amfani da ikonsa ya yi kāriya ta mu’ujiza a kowanne yanayi, babu shakka, Shaiɗan zai sami dalilin yi wa Jehobah zolaya kuma ya tuhumi gaskiyar ibadarmu ga Allah.—Ayuba 1:9, 10.

14. Waɗanne misalai suka nuna cewa Jehobah ba ya kāre dukan bayinsa a hanya iri ɗaya?

14 Har a zamanin Littafi Mai Tsarki, Jehobah bai yi amfani da ikonsa na kāriya ba ya kāre kowanne bawansa daga mutuwa. Alal misali, Hirudus ya kashe manzo Yaƙub a shekara ta 44 A.Z.; ba da jimawa ba bayan haka, aka ceci Bitrus daga “hannun Hirudus.” (Ayyukan Manzanni 12:1-11) Kuma Yohanna, ɗan’uwan Yaƙub, ya rayu fiye da Bitrus da kuma Yaƙub. Hakika, ba za mu yi tsammanin Allah zai kāre dukan bayinsa a hanya iri ɗaya ba. Ban da haka, “lokaci da sa’a” sukan sami kowannenmu. (Mai-Wa’azi 9:11) To, ta yaya Jehobah yake kāre mu a yau?

Jehobah Yana Ba da Kāriya ta Zahiri

15, 16. (a) Wane tabbaci ne da akwai cewa Jehobah ya kāre rukunin masu bauta masa a zahiri? (b) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah zai kāre bayinsa yanzu da kuma a lokacin “babban tsananin”?

15 Da farko, ka yi la’akari da batun kāriya ta zahiri. Masu bauta wa Jehobah za su yi tsammanin irin wannan kāriyar a rukuninsu. Idan ba haka ba, da mun zama abinci mai sauƙin samu ga Shaiɗan. Ka yi tunani game da wannan: Shaiɗan, “mai mulkin duniyar nan,” ba zai so wani abu ba sai dai ya kawar da bauta ta gaskiya. (Yohanna 12:31; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:17) Wasu gwamnatocin duniya masu iko suna hana mu aikin wa’azi kuma sun yi ƙoƙarin su shafe mu daga doron ƙasar gabaki ɗaya. Duk da haka, mutanen Jehobah sun kasance da ƙarfi kuma sun ci gaba da wa’azi ba tare da sanyin gwiwa ba! Me ya sa al’ummai masu ƙarfi sun kasa hana wannan ƙaramin rukuni na Kiristoci da kamar ba su da mai kāre su? Domin Jehobah ya kāre mu da fukafukansa masu ƙarfi ne!—Zabura 17:7, 8.

16 To, kāriya ta zahiri lokacin “babban tsananin” da yake zuwa fa? Bai kamata mu ji tsoron hukuncin Allah ba. Ban da ma haka, Jehobah “Allah yana iya ceton masu halinsa daga cikin gwaje-gwajensu. Allah ya san kuma yadda zai tsare masu mugunta har zuwa ranar shari’a.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:14; 2 Bitrus 2:9) Kafin nan, za mu iya kasancewa da tabbaci kullum game da abubuwa biyu. Na farko, Jehobah ba zai ƙyale a kau da bayinsa ba daga duniya. Na biyu, zai albarkaci waɗanda suke da aminci da rai madawwami a sabuwar duniyarsa—idan ya zama dole, ta tashin matattu. Ga waɗanda suka mutu, babu wajen kwanciyar rai kamar cikin tunanin Allah.—Yohanna 5:28, 29.

17. Ta yaya Jehobah yake kāre mu ta wurin Kalmarsa?

17 Har a yanzu ma, Jehobah yana kāre mu ta wurin ‘kalmarsa,’ wadda take da ƙarfin motsawa ta warkar da zukata kuma ta canja rayuwa. (Ibraniyawa 4:12) Ta wajen amfani da mizananta, a wasu ɓangare za a kāre mu daga rauni na zahiri. Ishaya 48:17 ta ce: “Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku.” Babu shakka, rayuwa cikin jituwa da Kalmar Allah za ta iya ta kyautata lafiyarmu ta jiki kuma ta ba mu tsawon rai. Alal misali, domin muna amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki mu guje wa fasikanci kuma mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazanta, muna guje wa ayyuka da ba su da tsabta da kuma halaye masu lahani da suke halaka rayuwan mutane da yawa marasa ibada. (Ayyukan Manzanni 15:29; 2 Korintiyawa 7:1) Muna godiya domin kāriyar Kalmar Allah!

Jehobah Yana Kāre Mu a Ruhaniya

18. Wace kāriya ta ruhaniya Jehobah ya yi mana tanadinta?

18 Mafi muhimmanci, Jehobah yana kāre mu a ruhaniya. Allahnmu mai ƙauna yana kāre mu daga haɗari ta wajen shirya mu da abubuwa da muke bukata domin mu jure wa gwaji kuma mu kāre dangantakarmu da shi. Da haka Jehobah yana kāre ranmu, ba kawai na ɗan shekaru ba amma na har abada. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da Allah ya yi tanadinsu da za su iya kāre mu a ruhaniya.

19. Ta yaya ruhun Jehobah zai sa mu iya jimre da gwaji da za mu fuskanta?

19 Jehobah “mai jin addu’o’i” ne. (Zabura 65:2) Sa’ad da matsi na rayuwa ya kasance kamar ya fi ƙarfinmu, buɗe masa zuciyarmu zai sa mu samu sauƙin abin. (Filibiyawa 4:6, 7) Ba zai cire mana gwajinmu ba ta mu’ujiza, amma wajen amsa addu’armu, zai ba mu hikima da za mu bi da shi. (Yakub 1:5, 6) Fiye da wannan, Jehobah yana ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda suka roƙe shi. (Luka 11:13) Wannan ruhu ne mai ƙarfi da zai sa mu iya jimre gwaji ko matsala da za mu fuskanta. Zai iya ba mu “cikakken iko da ya fi duka” mu jure har sai Jehobah ya cire dukan matsaloli masu azabtarwa a sabuwar duniya da ta yi kusa.—2 Korintiyawa 4: 7.

20. Ta yaya ikon kāriyar Jehobah za ta iya bayyana ta wajen ’yan’uwanmu masu bi?

20 Wani lokaci, ta wajen ’yan’uwanmu masu bi, ikon kāriyar Jehobah zai bayyana. Jehobah ya jawo mutanensa a dukan duniya don su zama “ ’yan’uwa.” (1 Bitrus 2:17; Yohanna 6:44) A tsakanin ’yan’uwancin, muna ganin tabbaci a zahiri na ikon ruhu mai tsarki na Allah, yana rinjayar mutane ga yin nagarta. Wannan ruhun yana ’ya’ya a cikinmu—kyawawa, halaye masu tamani da ya haɗa da ƙauna, kirki, da kuma nagarta. (Galatiyawa 5:22, 23) Saboda haka, sa’ad da muke wahala kuma wani ɗan’uwa mai bi ya motsa ya ba da shawara mai taimako ko kuma ya ƙarfafa mu, za mu yi godiya ga Jehobah domin wannan kāriyarsa.

21. (a) Wane abinci na ruhaniya Jehobah yake tanadinsa ta wajen “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (b) Kai kanka ka taɓa amfana daga tanadi na Jehobah na kāre mu a ruhaniya?

21 Jehobah ya yi tanadin wani abu kuma don ya ƙare mu: abinci na ruhaniya a kan kari. Domin ya taimake mu mu sami ƙarfi daga Kalmarsa, Jehobah ya umurci “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya ba da abinci na ruhaniya. Wannan ajin bawa mai aminci yana amfani da littattafai, haɗe da jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake!, da dandalinmu na jw.org da kuma taron Kirista domin ya ba mu ‘abinci a lokacinsa’—abin da muke bukata, lokacin da muke bukatarsa. (Matiyu 24:45) Ka taɓa jin wani abu a taron Kirista—a kalami, a jawabi, ko kuma a addu’a ma—da ya ba ka ƙarfi da kuma ƙarfafa da ka ke bukata? Wani talifi da aka buga a jaridunmu ya taɓa taɓa rayuwarka? Ka tuna, Jehobah yana yin dukan wannan tanadin domin ya kāre mu a ruhaniya.

22. A wace hanya Jehobah yake amfani da ikonsa koyaushe, kuma me ya sa yin hakan domin amfaninmu ne?

22 Babu shakka, Jehobah garkuwa ne “ga dukan masu neman wurin ɓuya a wurinsa.” (Zabura 18:30) Mun fahimci cewa ba ya yin amfani da ikonsa ya kāre mu daga dukan bala’i a yanzu. Amma, koyaushe yana amfani da ikonsa na kāriya ya tabbatar da nufinsa. A ƙarshe, abin da ya yi zai kasance domin albarkar mutanensa. Idan muka matso kusa da shi kuma muka kasance cikin ƙaunarsa, Jehobah zai ba mu dawwama ta kamiltaccen rai. Da wannan a zuci, za mu iya ɗaukan wahalar wannan tsari ‘mai-sauƙi ne kuma na ɗan lokaci.’—2 Korintiyawa 4:17.