BABI NA 46
Ruwa Ya Halaka Duniya—Zai Sake Faruwa Ne
KA TAƁA jin wani yana magana game da ƙarshen duniya?— A yanzu mutane da yawa suna magana game da shi. Wasu mutane suna tsammanin cewa za a halaka duniya a yaƙin mutane ta wajen bam na nukiliya. Kana tsammanin Allah zai ƙyale mutane su halaka wannan duniyar tamu kyakkyawa da kuma sama da taurarinta masu haske?—
Kamar yadda muka koya, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da ƙarshen duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya ma tana wucewa.” (1 Yohanna 2:17) Kana tsammanin ƙarshen duniya ƙarshen doron ƙasa ne?— Littafi Mai Tsarki ya ce Allah Ya halicci duniya domin “wurin zama,” domin mutane su zauna a ciki kuma su more ta. (Ishaya 45:18) Zabura 37:29 ta ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki ya ce duniya za ta dawwama.—Zabura 104:5; Mai-Wa’azi 1:4.
To, idan ƙarshen duniya ba ya nufin ƙarshen doron ƙasa, menene yake nufi?— Za mu fahimta idan muka lura da abin da ya faru a zamanin Nuhu. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Duniya wadda ta ke a sa’an nan, yayinda ruwa ya sha kanta [ko ya yi ambaliya], ta halaka.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; 2 Bitrus 3:6.
Da akwai wanda ya rayu ne a ƙarshen duniya bayan rigyawa ko kuma ambaliyar, a zamanin Nuhu?— Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya “ceci Nuhu mai-shelan adalci, tare da waɗansu bakwai, sa’anda ya kawo rigyawa bisa duniya ta masu-fajirci.”—2 Bitrus 2:5.
To, mecece ce duniya da ta halaka? Doron ƙasa ne, ko kuma miyagun mutane?— Littafi Mai Tsarki ya ce “duniya ta masu-fajirci” ce. Ka lura an kira Nuhu “mai-shelan adalci.” Me kake tsammanin yake wa’azinsa?— Nuhu ya yi wa mutane ne gargaɗi game da “duniya wadda ta ke sa’an nan.”
Sa’ad da Yesu ya yi magana game da wannan gagarumar ambaliya, ya gaya wa almajiransa game da abin da mutanen suke yi kafin ƙarshen ya kai. Ga abin da ya ce musu: “Kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna aurarwa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har ran da Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” Yesu ya ce mutane za su riƙa yin abubuwa irin nasu kafin wannan duniyar ta halaka.—Tafiyar tsutsa tamu ce; Matta 24:37-39.
Babi na 10 na wannan littafin, ka tuna abin da waɗannan mutane suka yi?— Wasu mutane masu ƙeta ne kuma suna nuna fin ƙarfi. In ji Yesu, wasu kuma da yawa ba su saurari Nuhu ba sa’ad da Allah ya aike shi ya yi musu wa’azi.
Kalmomin Yesu sun nuna cewa za mu iya koyon darasi daga abin da mutane suke yi kafin Ambaliyar. Daga karatunSa’ad da lokaci ya yi, Jehovah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka miyagun mutane da ambaliya. Ruwan zai sha kan dukan duniya har da duwatsu. Jehovah ya gaya wa Nuhu ya gina babban jirgi. Jirgin kamar babban akwati ne, kamar yadda za ka gani idan ka juya zuwa hoton a shafi na 238.
Allah ya gaya wa Nuhu ya gina babban jirgi da zai ɗauki iyalinsa da kuma dabbobi da yawa a cikinsa. Nuhu da iyalinsa sun yi aiki sosai. Sun sassare manyan itatuwa, suka yi amfani da su, suka fara gina jirgin. Kafin su gama jirgin ya ɗauki shekaru masu yawa domin jirgin yana da girma.
Ka tuna abin da Nuhu kuma yake yi a lokacin da yake gina jirgin?— Yana wa’azi, yana yi wa mutane gargaɗi game da Ambaliya da take zuwa. Da akwai wanda ya saurara ne? Babu wanda ya saurara sai dai iyalin Nuhu kawai. Sauran sun shagala kawai cikin wasu ayyuka. Ka tuna abin da Yesu ya ce suna yi?— Sun shagala cikin ci da sha da aure. Suna ganin su ba miyagun mutane ba ne, kuma ba su ba da lokaci ba su saurari Nuhu. Bari mu ga abin da ya faru da su.
Bayan Nuhu da iyalinsa suka shiga cikin jirgin, Jehovah ya rufe ƙofar jirgin. Mutanen da suke waje har ila ba su yarda cewa Ambaliyar za ta zo ba. Amma farat ɗaya, sai ruwa ya fara zubowa daga sama! Ba ruwan sama ba ne kawai. Ruwa ne mai ƙarfi! Ba da daɗewa Matta 24:39; Farawa 6:5-7.
ba ruwan ya zama kamar babban kogi, yana gurnani. Ya tuttuge itatuwa ya tutture manyan duwatsu kamar a ce ƙanana ne. Mutane da suke waje da jirgin fa?— Yesu ya ce: “Rigyawar ta zo ta kwashe su duka.” Dukan mutane da suke waje suka mutu. Me ya sa?— Kamar yadda Yesu ya ce, ‘ba su farga ba.’ Ba su saurara ba!—Ka tuna cewa, Yesu ya ce abin da ya faru da waɗannan mutane darasi ne wa zamaninmu. Wane darasi za mu koya?— An halaka mutane ba domin kawai miyagu ba ne amma kuma domin sun shagala wajen ayyukansu ba su ba da lokaci su koyi game da Allah ba da kuma abin da zai yi. Muna bukatar mu mai da hankali kada mu zama kamarsu, ko ba haka ba ne?—
Kana tsammanin Allah zai sake halaka duniya da ambaliya?— A’a, Allah ya yi alkawari cewa ba zai yi haka ba kuma. Ya ce: “Na sa bakana a cikin hadari, za ya zama shaida.” Jehovah ya ce bakan za ta zama shaida cewa “ruwaye kuma ba za su ƙara zama rigyawa wadda za ta halaka dukan nama ba.”—Farawa 9:11-17.
Lallai za mu iya tabbata cewa Allah ba zai sake halaka duniya ba da Ambaliya. Duk da haka, kamar yadda muka gani, Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da ƙarshen duniya. Sa’ad da Allah zai halaka wannan duniyar, waye Allah zai cece shi?—
Mutane ne da suke yin wasu abubuwa da ba sa so su koya game da Allah? Waɗanda suka shagala ne ba su da lokacin yin nazarin Littafi Mai Tsarki? Me kake tsammani?—Muna so mu kasance tsakanin waɗanda Allah zai cece su, ko ba haka ba?— Ba zai zama abin sha’awa ba idan iyalinmu ta zama kamar ta Nuhu don Allah ya ceci dukanmu?— Idan za mu tsira wa ƙarshen wannan duniyar, muna bukatar mu fahimci yadda Allah zai halaka wannan duniyar kuma ya kawo sabuwar duniyarsa ta adalci. Bari mu ga yadda zai yi haka.
Littafi Mai Tsarki ya ba mu amsa a Daniel sura 2, aya ta 44. Wannan nassin yana magana ne game da zamaninmu, sa’ad da ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”
Ka fahimci wannan?— Littafi Mai Tsarki ya ce gwamnatin Allah za ta halaka dukan gwamnatin mutane. Me ya sa?— Domin ba sa yi wa Wanda Allah ya naɗa Sarki biyayya. Wanene wannan?— Yesu Kristi!
Jehovah Allah yana da ikon ya faɗi irin gwamnatin da za ta yi sarauta, kuma ya zaɓi Ɗansa Yesu, ya zama Sarki. Ba da daɗewa ba Sarki da Allah ya naɗa, Yesu Kristi, zai yi ja-gora wajen halaka dukan gwamnatocin wannan duniyar. Littafi Mai Tsarki, a Ru’ya ta Yohanna sura 19, aya ta 11 da 16, ta kwatanta shi sa’ad da yake halaka su, kamar yadda kake gani a wannan hoton. A cikin Littafi Mai Tsarki, yaƙin Allah da zai halaka dukan gwamnatocin duniya ana kiran shi Har–Magedon, ko kuma Armageddon.
Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Hakika, Armageddon yaƙin Allah ne, kuma zai yi amfani da Yesu Kristi ya ja-goranci rundunar samaniya wajen yaƙin. Yaƙin Armageddon ya yi kusa ne? Bari mu ga yadda za mu sani.
Allah ya ce Mulkinsa zai halaka gwamnatocin mutane. Amma ya ce mana ne mu yi haka?— A’a, a cikin Littafi Mai Tsarki, an kira Armageddon “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (Bari mu karanta tare sa’ad da Allah ya halaka dukan miyagu, kuma ya ceci waɗanda suka bauta masa, a Misalai 2:21, 22; Ishaya 26:20, 21; Irmiya 25:31-33; da kuma Matta 24:21, 22.