DARASI NA 51
Ta Yaya Abin da Kake Fada Zai Faranta wa Jehobah Rai?
Jehobah ya halicce mu da baiwa mai kyau, wato baiwar yin magana. Shin, ya damu da yadda muke amfani da wannan baiwar? Ƙwarai da gaske! (Karanta Yakub 1:26.) Ta yaya za mu yi amfani da baiwar yin magana da Jehobah ya ba mu don mu faranta masa rai?
1. Ta yaya za mu yi amfani da baiwar yin magana?
Littafi Mai Tsarki ya ce, “ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna.” (1 Tasalonikawa 5:11) Ka san wasu mutane da suke bukatar ƙarfafawa? Me za ka yi don ka taimaka musu? Ka tabbatar musu da cewa ka damu da su. Za ka iya gaya musu abubuwan da suke yi da kake so. Akwai wata aya da ka sani da za ka iya ƙarfafa wani da ita? Akwai nassosi da yawa da za ka iya zaɓa. Ka tuna cewa yadda ka faɗi wani abu zai iya ƙarfafa mutane sosai. Saboda haka, ka yi ƙoƙari ka riƙa yin magana yadda ya dace.—Karin Magana 15:1.
2. Wace irin magana ce bai kamata mu yi ba?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada wani ƙazamin zance ya fita daga bakinku.” (Karanta Afisawa 4:29.) Hakan yana nufin cewa ba za mu yi maganar banza, ko mu faɗi abin da zai ɓata wa wani rai da gangan ba. Ƙari ga haka, wajibi ne mu guji gulma da kuma ɓata sunan mutane.—Karanta Karin Magana 16:28.
3. Me zai taimaka mana mu riƙa maganar da za ta ƙarfafa mutane?
Sau da yawa abin da muke faɗa yakan nuna abin da ke zuciyarmu ko abin da ke damunmu. (Luka 6:45) Saboda haka, ya kamata mu riƙa tunanin abubuwa masu kyau, kamar abin da ke daidai, da abin da ke da tsabta, da abin da ke sa mu ƙaunaci mutane, da abin da ya isa ya kawo yabo. (Filibiyawa 4:8) Don mu mai da hankali a kan waɗannan abubuwan, wajibi ne mu zaɓi nishaɗi da abokanmu da kyau. (Karin Magana 13:20) Yana da kyau mu yi tunani sosai kafin mu yi magana. Ka yi tunanin yadda mutane za su ji game da abin da ka faɗa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar da an yi da rashin tunani tana sa rauni kamar sokin takobi, amma harshe mai hikima yakan kawo warkewa.”—Karin Magana 12:18.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi yadda za mu riƙa magana yadda zai faranta ran Jehobah kuma ya ƙarfafa mutane.
4. Ka lura da abin da kake faɗa
A wasu lokuta, mukan faɗi abubuwan da muke yin da-na-sani daga baya. (Yakub 3:2) Ku karanta Galatiyawa 5:22, 23, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Waɗanne cikin halayen da aka ambata a ayoyin ne za ka yi addu’a ka kasance da su sa’ad da kake magana? Ta yaya halayen nan za su taimaka maka?
Ku karanta 1 Korintiyawa 15:33, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Ta yaya abokanka ko irin nishaɗin da kake yi zai iya shafan abin da kake faɗa?
Ku karanta Mai-Wa’azi 3:1, 7, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Wane lokaci ne zai dace ka yi shiru ko ka ɗan jira kafin ka yi magana a lokacin da ya dace?
5. Ka riƙa faɗin abubuwa masu kyau game da mutane
Ta yaya za mu guji zagin mutane ko kuma yi musu baƙar magana? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
-
Me ya sa ɗan’uwan da ke bidiyon yake so ya canja yadda yake magana game da mutane?
-
Mene ne ya yi don ya gyara halinsa?
Ku karanta Mai-Wa’azi 7:16, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke so mu yi baƙar magana game da wani?
Ku karanta Mai-Wa’azi 7:21, 22, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Ta yaya ayoyin nan za su taimaka maka kada ka yi fushi idan wani ya yi maganar da ba ta dace ba game da kai?
6. Ka riƙa daraja iyalinka sa’ad da kake yi musu magana
Jehobah yana so mu riƙa magana da iyalinmu yadda za mu nuna muna ƙaunar su. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
-
Mene ne zai taimaka maka ka yi wa iyalinka magana a hanyar da za ta nuna kana ƙaunar su?
Ku karanta Afisawa 4:31, 32, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Wace irin magana ce take kawo zaman lafiya a iyali?
Jehobah ya faɗi yadda yake ji game da Ɗansa, wato Yesu. Ku karanta Matiyu 17:5, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Ta yaya za ka yi koyi da Jehobah a yadda kake magana da iyalinka?
WASU SUN CE: “Duk abin da na ga dama nake faɗa. Ba ruwana da yadda mutane suke ji game da abin da na faɗa.”
-
Ka yarda da hakan? Me ya sa?
TAƘAITAWA
Abin da muke faɗa yakan ƙarfafa mutane ko kuma ya ɓata musu rai. Ya kamata mu yi tunani sosai game da abin da za mu faɗa, lokacin da za mu faɗe shi da kuma yadda za mu faɗe shi.
Bita
-
A waɗanne hanyoyi ne za ka yi amfani da furucinka don ka taimaka wa mutane?
-
Wace irin magana ce bai kamata mu yi ba?
-
Me zai taimaka mana mu riƙa faɗin abubuwan da za su ƙarfafa mutane?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da zai taimaka mana mu iya yin magana yadda zai ƙarfafa mutane.
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da zai taimaka muku ku guji yin baƙar magana.
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda za ku guji yin gulma.
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda Jehobah ya taimaka ma wani mutum ya daina yin baƙar magana.
“Na Soma Tunani Sosai Game da Inda Na Nufa A Rayuwa” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2013)