LABARI NA 82
Mordekai Da Esther
BARI mu ɗan koma baya ’yan shekaru kafin Ezra ya tafi Urushalima. Mordekai da Esther su ne Isra’ilawa mafiya martaba a masarautar Farisa. Esther sarauniya ce, ɗan kawunta kuma Mordekai shi ne mataimakin sarki. Bari mu ga yadda haka ya faru.
Iyayen Esther sun rasu sa’ad da take ’yar ƙarama saboda haka Mordekai ne ya yi renonta. Ahasuerus sarkin Farisa yana da fada a birnin Shushan, Mordekai yana ɗaya daga cikin bayinsa. Wata rana matar sarki mai suna Vashti ba ta yi masa biyayya ba, saboda haka sarkin ya zaɓi sabuwar mace ta zama sarauniya. Ka san matar da ya zaɓa? Hakika, Esther ce kyakkyawa.
Ka ga wannan mutumin mai fahariya da mutane suke durƙusa masa? Wannan shi ne Haman. Mutum ne mai ɗaukaka a Farisa. Haman yana so Mordekai wanda kake gani yana zaune a nan ya durƙusa masa. Amma Mordekai ya ƙi. Yana ganin bai dace ba ya durƙusa wa wannan mugun mutumin. Wannan ya sa Haman ya yi fushi sosai. Za ka ga abin da zai yi.
Haman ya yi wa sarki ƙarya game da Isra’ilawa. Ya ce: ‘Miyagun mutane ne, da ba sa bin dokokinka. Ya kamata a kashe su.’ Ahasuerus bai san cewa matarsa Esther Ba’isra’iliya ba ce. Saboda haka ya saurari Haman, kuma ya kafa doka cewa a wata rana da ya ƙayyade za a kashe duka Isra’ilawa.
Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dokar ya yi fushi sosai. Ya aika wa Esther saƙo: ‘Ki gaya wa sarki kuma ki roƙe shi ya cece mu.’ Dokar Farisa ta hana zuwa wurin sarki, sai dai idan sarki ne ya gayyace ka. Amma Esther ta tafi ba tare da an gayyace ta ba. Sarki ya miƙa mata sandarsa ta zinariya, kuma hakan yana nufin kada a kashe ta. Esther ta gayyaci sarki da kuma Haman zuwa babbar liyafa. A nan sarki ya tambayi Esther me take so ya yi mata. Ta ce za ta gaya masa idan shi da Haman za su sake zuwa cin abinci gobe.
Sa’ad da suke cin abinci Esther ta gaya wa sarki: ‘Za a kashe ni da mutanena.’ Sarki ya yi fushi. ‘Waye yake so ya yi irin wannan abu?’ ya yi tambaya.
‘Mutumin, kuma abokin gaban, shi ne Haman!’ In ji Esther.
Sarki ya yi fushi sosai. Ya ba da doka cewa a kashe Haman. Daga baya sarki ya naɗa Mordekai ya zama mataimakinsa. Sai Mordekai ya sa aka kafa sabuwar doka da ta ƙyale Isra’ilawa su kāre kansu a ranar da aka zo za a kashe su. Domin Mordekai ya zama mutum mai martaba yanzu, mutane da yawa suka taimaki Isra’ilawan suka tsira daga hannun abokanan gabansu.
Littafin Littafi Mai Tsarki na Esther.