Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Shin Allah ya halicce mu domin mu riƙa mutuwa ne?

Nassi: R. Yoh 21:4

Abin da Za Ka Ce: Wannan mujallar Hasumiyar Tsaro ta bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da rai da kuma mutuwa.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Me ya sa mutane suke shan wahala sosai a duniya?

Nassi: 1Yo 5:19

Gaskiya: Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar.

YAYA AKE GUDANAR DA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?

Abin da Za Ka Ce: Shaidun Jehobah suna tattauna Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta, kuma suna amsa tambayoyi kamar su: Me ya sa muke shan wahala? Me zai sa iyali ta yi farin ciki? Wannan gajeren bidiyon ya nuna yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. [Ka nuna bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki?] Za mu riƙa tattauna wannan littafin. [Ka nuna masa ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su kuma idan zai yiwu ku tattauna littafin.]

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.