Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Koya Musu Su Rika Bauta wa Jehobah

Ku Koya Musu Su Rika Bauta wa Jehobah

Mun lura cewa masu shelan da aka taimaka musu tun daga farko su kasance da ƙwazo a wa’azi suna ƙwarewa sosai. (Mis 22:6; Fib 3:16) Ga wasu abubuwan da za ku yi don ku taimaka wa ɗalibanku su ƙware a yin wa’azi:

  • Ku soma koya musu yadda ake wa’azi da zarar sun zama masu shela. (km 8/15 shafi na 1) Ku sa su ga muhimmanci fita wa’azi kowane mako. (Fib 1:10) Ku gaya musu abubuwa masu kyau game da yankin da kuke wa’azi. (Fib 4:8) Ku ƙarfafa su su riƙa fita wa’azi tare da mai kula da rukunin masu wa’azi da kuma wasu masu shela da suka ƙware don su amfana.​—Mis 1:5; km 10/12 6 sakin layi na 3

  • Bayan ɗalibin ya yi baftisma, ku ci gaba da ƙarfafa shi da kuma koyar da shi a wa’azi musamman ma idan bai kammala nazarin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” ba.​—km 12/13 shafi na 7

  • Idan kuna wa’azi tare da sabon mai shela, ku yi amfani da gabatarwa mai sauƙi. Bayan kun saurari wa’azinsa, ku yaba masa. Ku ba shi shawarwarin da za su taimaka masa ya ƙware sosai.​—km 5/10 shafi na 7